Ba zan lamunci rashin da’a ba – Sabon gwamna na shirin hukunta wasu ma’aikatan gwamnati

Ba zan lamunci rashin da’a ba – Sabon gwamna na shirin hukunta wasu ma’aikatan gwamnati

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum a ranar Juma’a, 31 ga watan Mayu ya kai ziyarar bazata sakatariyar gwamnatin jihar, inda ya ga ma’aikata uku kacal ne suka isa wajen aiki da misalin karfe 8:30am.

“Malalaci bai da abinci, mu iso nan da misalin karfe 8:30, mun tarar da ma’aikata uku ne kacal sannan a yanzu karfe 9:30 muna da ma’aikata 135 ne kawai suka iso wajen aiki.”

Farfesa Zulum ya bayyana hakan bayan ziyarar da ya kai sakatariyar jihar da ke Maiduguri, ya kuma bayyana cewa a shirye gwamnatinsa take ta biya ma’aikata, don haka ya zama dole suma su yi adalci wajen aiki.

“Za a yanta ma’aikata masu kwazo da jajircewa. Nayi umurni da a biya ma’aikatan 135 da suka iso wajen aiki kudin hutu ba tare da bata lokaci ba. Za mu tabbatar da ganin cewa wadannan ma’aikata sun samu duk wani hakki nasu,” Zulum yayi gargadi.

KU KARANTA KUMA: Aiki kawai: Gwamna Zulum yayi umurnin biyan bashin albashi da fansho ba tare da bata lokaci ba

Yayi gargadin cewa ba zai lamunci rashin da’a ba sannan za a hukunta ma’aikata marasa da’a.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel