Sabon gwamna ya fara da biyan ma’aikatan albashinsu

Sabon gwamna ya fara da biyan ma’aikatan albashinsu

Kwanaki biyu bayan darewarsa madafan iko, Sabon gwamnan jahar Bauchi, Abdulkadir Bala Muhammad ya bayar da umarnin biyan albashin ma’aikatan jahar ba tare da bata lokaci ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin gwamnan, Mukhtar Mohammed Gidado ne ya bayyana haka a ranar Juma’a, 31 ga watan Mayu, inda yace gwamnan ya umarci a gaggauta biyan albashin don rage ma ma’aikata radadi.

KU KARANTA: Sanata Bala kaura ya yi nade naden farko a matsayin gwamnan Bauchi

Haka zalika sanarwar ta kara da umartar ofishin akantan jahar daya tabbata ya biya ma’aikatan albashinsu daga ranar Juma’a zuwa ranar Litinin, 3 ga watan Yuni, musamman duba da karatowar bikin Sallah karama.

Sai dai sabon gwamnan ya umarci kada a biya ma’aikatan da tsohuwar gwamnatin jahar ta sallama daga aiki a watan Afrilu da watan Mayu, sa’annan ya bada tabbacin gwamnatinsa ba za tayi wasa da hakkokin ma’aikata.

Daga karshe sabon gwamnan ya yi kira ga ma’aikatan dasu kasance masu nuna jajircewa da kwazo a bakin aikinsu don tabbatar an samar da ingantaccen tsarin aikin gwamnati a jahar Bauchi.

A wani labarin kuma, Gwamna Bala Mohammed Kauran Bauchi yayi sabbin nade nade na farko a gwamnatinsa, inda ya nada Muhammad Baba a matsayin sakataren gwamnatin jahar Bauchi, da kuma Dakta Abubakar Kari a matsayin shugaban ma’aikatan fadar gwamnati.

Sauran mukaman da Gwamna Bala ya nada sun hada da Alhaji Bashir Yau a matsayin mataimakin shugaban ma’aikatan fadar gwamnati da zai yi aiki a ofishin mataimakin gwamna Alhaji Baba Tela.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel