Yanzu Yanzu: Sabon gwamnan Oyo ya soke kungiyar NURTW

Yanzu Yanzu: Sabon gwamnan Oyo ya soke kungiyar NURTW

Gwamnatin Jihar Oyo, a ranar Juma'a ta haramta aikace-aikacen kungiyar direbobi na kasa NURTW reshen jihar.

Hakan ya biyo bayan tabarbarewar tsaro da ya faru sakamakon rikici da ya barke tsakanin bangarori biyu na kungiyar a wasu unguwanni a Ibadan, babban birnin jihar.

Babban dogarin gwamnan, Mr Bisi Ilaka ya shaidawa manema labarai cewa ofishin gwamnan ta haramta dukkan ayyukan kungiyar a jihar.

DUBA WANNAN: Diyar Atiku ta ce ba za ta taba mantawa da mulkin APC ba

Ilaka ya ce an dauki matakin ne bayan ganawa da masu ruwa da tsaki a fannin da suka hada da shugabanin hukumomin tsaro a jihar da jami'an gwamnati.

Ilaka ya bukaci al'ummar jihar su cigaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda suka saba.

A ranar Alhamis, Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Olugbenga Fadeyi ya shaidawa Punch cewa an kama mambobin NURTW guda shida a tashar mota saboda tayar da rikici a ranar Laraba da Alhamis.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel