Tsuntsu daga sama: Sabon gwamnan Borno ya yiwa wasu ma’aikata 135 sha tara ta arziki

Tsuntsu daga sama: Sabon gwamnan Borno ya yiwa wasu ma’aikata 135 sha tara ta arziki

Sabon gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya kai ziyarar gani da ido sakatariyar Musa Usman na jihar, inda ya tarar da ma’aikata 135 kacal cikin kusan su 12,000. Saboda haka ya umurci Shugaban ma’aikata da ya biya su kudin da ake biyan wadanda suka tafi hutu.

Da misalin karfe 8:30 da ya isa wajen ma’aikata uku kadai ya tarar sai dai yawansu ya karu zuwa 135 da misalin 9:45 kafin ya bar wajen

Gwamnan ya wallafa hakan a shafinsa na Facebook inda yake cewa: “Na umurci Shugaban ma’aikata da yayi gaggawan biyan kudin hutu ga ma’aikata 135 da na tarar a ofis a yau Juma’a, 31 ga watan Mayu a lokacin rangajin nazari da na yi a sakatariyar Musa Usman.

"Da misalin karfe 8:30, ma’aikata uku kadai na tarar, zuwa 9:45, yawansu ya karu zuwa 135. Kuma adadin ma’aikatan da ke aiki a sakatariyar ya kai kimanin 12,000."

KUKARANTA KUMA: Eid Al Fitr: UAE ta kafa kwamitin neman wata domin tabbatar da karshen Ramadan

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa, Gwamna Babangida Zulum na jihar Borno, a jiya Alhamis, 30 ga watan Mayu, yayi umurnin biyan albashi da basussukan albashi da fansho na ma’aikatan gwamnatin da aka tantance da wadanda ba a tantance ba kafin bikin karamar sallah.

Gwamnan ya bada umurnin ne a lokacin da shugaban kungiyar kwadago, Bulama Abiso, ya jagoranci sauran mambobin kungiyar a ziyarar da suka kai mishi a gidan Gwamnati, a Maiduguri, babbar birnin jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel