Aiki kawai: Gwamna Zulum yayi umurnin biyan bashin albashi da fansho ba tare da bata lokaci ba

Aiki kawai: Gwamna Zulum yayi umurnin biyan bashin albashi da fansho ba tare da bata lokaci ba

Gwamna Babangida Zulum na jihar Borno, a jiya Alhamis, 30 ga watan Mayu, yayi umurnin biyan albashi da basussukan albashi da fansho na ma’aikatan gwamnatin da aka tantance da wadanda ba a tantance ba kafin bikin karamar sallah.

Gwamnan ya bada umurnin ne a lokacin da shugaban kungiyar kwadago, Bulama Abiso, ya jagoranci sauran mambobin kungiyar a ziyarar da suka kai mishi a gidan Gwamnati, a Maiduguri, babbar birnin jihar.

Ku tuna a baya cewa, Kashim Shettima, fiye da shekaru uku da suka gabata ya gabatar da tsarin tantance ma’aikatan gwamnati, wanda yayi sanadiyan tsayar da albashin dubban ma’aikatan gwamnati wanda kwamitin da Mista Bako ke jagoranta ke dauke da alhakin hakan.

Domin sanya farin ciki a fuskokin ma’aikata da kuma yan fanshon da lamarin ya shafa, Zulum ya umurci sakatarorin ma’aikatu da shuwagabannin hukumomin gwamnati da su yi gaggawan hada jerin sunayen ma’aikatansu wadanda lamarin ya shafa, a kawo teburin shi kafin ranar 3 ga watan Yuli, 2019 domin sa hannu da kuma biya kafin bikin sallah mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Ku mika kanku ga EFCC – Fayose ga Okorocha da Amosun

A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto cewa Sabon gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya kai ziyarar gani da ido sakatariyar Musa Usman na jihar, inda ya tarar da ma’aikata 135 kacal cikin kusan su 12,000. Saboda haka ya umurci Shugaban ma’aikata da ya biya su kudin da ake biyan wadanda suka tafi hutu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel