Shugabanin kananan hukumomi a Oyo sun ki yin biyaya ga umurin sabon gwamna

Shugabanin kananan hukumomi a Oyo sun ki yin biyaya ga umurin sabon gwamna

Shugabanin kananan hukumomi a jihar Oyo sun sha alwashin cigaba da kasancewa a ofisoshinsu duk da sanarwar rushe su da sabon gwamnan jihar, Seyi Makinde ya yi.

Shugaban kungiyar ciyamomin kananan hukumomi (ALGON) na jihar, Ayodeji Abass-Alesinloye wanda ya jagoranci sauran ciyamomi 15 zuwa ofishin kungiyar 'yan jarida na kasa NUJ, ya ce gwamnan ya rushe su ne duk da cewar kotu ta dakatar da shi daga aikata hakan.

A jawabinsu, shugabanin kananan hukumomin sun ce sallamar su daga aiki da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya yi ya sabawa demokradiyya kuma ba bisa ka'ida bane.

Shugabanin kananan hukumomi a Oyo sun ki yin biyaya ga umurin sabon gwamna

Shugabanin kananan hukumomi a Oyo sun ki yin biyaya ga umurin sabon gwamna
Source: UGC

DUBA WANNAN: Diyar Atiku ta ce ba za ta taba mantawa da mulkin APC ba

Abass-Alesinloye ya cigaba da cewa yanayin da gwamnan ya bayar da sanarwar sallamar su daga aiki ya yi kamanceceniya da irin kama karyar da shugabanin mulkin soji ke yi.

Ya ce, "Abin takaici ne a demokradiyya hakan ya rika faruwa. An bayar da sanarwar rushe mu kasa da sa'o'i 12 bayan an rantsar da gwamna Makinde."

Shugabanin kananan hukumomin sun sha alwashin cigaba da kasancewa a ofisoshinsu.

Duk da cewa gwamnan ta bakin shugaban ma'aikatansa, Cif Bisi Ilaka a yammacin ranar Laraba ya bayar da umurnin 'rushe dukkan shugabanin kananan hukumomi nan ta ke."

Ya ce ciyamomin kananan hukumomin su mika aiki ga shugabanin sashin mulki ko ma'aikatan da suka fi mukami a hukumomi da ma'aikatunsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel