Eid Al Fitr: UAE ta kafa kwamitin neman wata domin tabbatar da karshen Ramadan

Eid Al Fitr: UAE ta kafa kwamitin neman wata domin tabbatar da karshen Ramadan

Tarayyar kasar Larabawa (UAE) ta kafa kwamitin neman kwata domin su gano farkon watan Shawwal, wanda shine zai kawo karshen Ramada da kuma fara Eid-el-Fitr.

Ministan shari’an kasar, Sultan Bin Saeed Al badi, ya bayyana cewa kwamitin zata gana a karkashin jagorancinsa tare da wasu manyan jami’ai, bayan sallar Maghrib a ranar Litinin, 3 ga watan Yuli (29 ga Ramadan) a sashin shari’a na Abu Dhabi.

Ministan ya kuma yi kira ga kotunan shari’a a fadin kasar das u nemi jinjirin wata sannan su sanar da kwamitin idan aka gani.

Eid Al Fitr: UAE ta kafa kwamitin neman wata domin tabbatar da karshen Ramadan

Eid Al Fitr: UAE ta kafa kwamitin neman wata domin tabbatar da karshen Ramadan
Source: UGC

Idan ba a ga watan ba, washegarin ranar, Talata, 4 ga watan Yuni, za a yi azumin Ramadana 30. Idan kuma aka ga wata, washegari, 4 ga watan Yuni zai kama 1 ga Shawwal, ranar kaaramar Sallah.

KU KARANTA KUMA: Kasafin kudin 2019: Buhari zai kashe N1bn a tafiye-tafiye

A baya Legit.ng ta rahoto cewa wata kotu a Jigawa a ranar Talata, 28 ga watan Mayu ta yanke wa wani matashi mai suna Ibrahim Ismaila hukuncin shan bulala 40 saboda karya azuminsa da yayi a bainar Jama’a ba tare da dalili ba kuma da rana tsaka.

Alkalin kotun, Safiyanu Ya’u ya yanke wa Isma’il wannan hukunci ne bayan hukumar Hisba ta kama shi yana shan mangoro baro-baro a bainar jama’a alhalin kowa na Azumi da gangan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel