Ku mika kanku ga EFCC – Fayose ga Okorocha da Amosun

Ku mika kanku ga EFCC – Fayose ga Okorocha da Amosun

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya shawarci taakwarorinsa na jihohin Imo da Ogun, Rochas Okorocha da Ibikunle Amosun da su mika kansu ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC).

Fayose, a shafinsa na twitter ya bukaci tsohon gwamnan Imo da ya yi koyi dashi sannan ya mika kansa ga hukumar yaki da rashawar. Ya kuma bayyana cewa kada EFCC ta dauke ido daga kan Amosun.

Da yake bayyana cewa yana ta zuba idon ganin irin wannan rana, Fayose ya bayyana cewa kofa a bude take domin Okorocha ya zo ya hadu dashi.

Ku mika kanku ga EFCC – Fayose ga Okorocha da Amosun

Ku mika kanku ga EFCC – Fayose ga Okorocha da Amosun
Source: UGC

KU KARANTA KUMA: Osinbajo ya jinjinawa limamin da ya ceci rayukan Kiristoci 300 a masallaci

Da farko dai mun samu wani labari da ke ta yawo kan cewa Jami'an hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arzikin kasa (EFCC) sun dira a Ogboko tare da kama tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, matar sa, Nkechi Okorocha, 'ya'yansa; Gerald Okorocha da Okey Okorocha.

Kazalika hukumar ta garkame jami'ar sa mai suna 'Eastern University' dake garin Ogboko. Tun kafin ya mika mulki, gwamna Rochas ya dade yana korafin cewar hukumar EFCC na gudanar da bincike a kansa tare da shirya yadda zasu kama shi da zarar ya mika mulki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel