Talauci ya tsananta a Najeriya karkashin mulkin Buhari - The Economist

Talauci ya tsananta a Najeriya karkashin mulkin Buhari - The Economist

Jaridar Economist ta yi bitar yadda al'amurra suka kasance a karkashin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari karo na farko inda ta ce talauci ya karu a Najeriya cikin shekaru hudu na mulkinsa.

A cikin kasidar da jaridar da wallafa a shafinta na Intanet a ranar Alhamis, ta ce tattalin arzikin Najeriya ya tsaya wuri guda kamar amalanken da akayi watsi da shi hakan yasa kudaden da 'yan Najeriya ke samu ya ragu daga shekarar 2015 zuwa 2019.

Jam'iyyun adawa karkashin jagorancin jam'iyyar PDP sun amince da rahoton da jaridar ta wallafa inda suka ce rahoton ya sake tabbatar da hasashen da su keyi na cewa Buhari bashi da kwarewar da zai tafiyar da Najeriya yadda ya dace.

Talauci ya karu a Najeriya a mulkin Buharo karo na farko - Economist

Talauci ya karu a Najeriya a mulkin Buharo karo na farko - Economist
Source: Twitter

Sun shawarci 'yan Najeriya su kasance cikin shiri domin za su fuskanci wahalhalu a cikin shekaru hudu da Buhari zai yi mulkinsa karo na biyu da za ta fara daga ranar 29 ga watan Mayun 2019.

DUBA WANNAN: Diyar Atiku ta ce ba za ta taba mantawa da mulkin APC ba

A cikin rahoton na Economist, ta ce idan akayi la'akari da hasashen Bankin Bayar da Lamuni na Duniya, IMF, "kudaden da mafi yawancin 'yan Najeriya ke samu ba zai karu ba a cikin shekaru shida masu zuwa."

Wani bangare na rahoton ya ce, "Tattalin arzikin Najeriya ya tsaya cak kamar kurar da akayi watsi da ita. Kudaden da 'yan Najeriya ke samu suna raguwa cikin shekaru hudu da suka gabata; IMF na ganin kudaden da 'yan kasar ke samu ba zai karu ba cikin shekaru shida masu zuwa.

"'Yan Najeriya kimanin miliyan 94 suna rayuwa a kan kudi kasa da Naira 684 a kowanne rana kuma kullum adadin mutanen karuwa ya keyi.

"A shekarar 2030, kashi 1 cikin hudu na 'yan Najeriya za su kasance cikin talauci kuma adadin na karuwa."

The Economist ta ce tattalin arzikin zai inganta idan gwamnatin Najeriya ta kara farashin man fetur duba da cewa NNPC ne ke sayo man fetur daga kasashen waje kuma ta sayar kasa da kudin da ta sayo saboda biyan kudin tallafi.

Rahoton ya ce 'yan siyasa ba su kula al'umma sai lokacin zabe ya yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel