Yanzu Yanzu: Shugaban PENGASSAN na kasa ya mutu

Yanzu Yanzu: Shugaban PENGASSAN na kasa ya mutu

Shugaban kungiyar manyan ma'aikatan man fetur da iskar gas na Najeriya wato PENGASSAN, Mr Francis Johnson ya mutu kamar yadda Punch ta tabbatar.

Johnson ya rasu ne da asubahin ranar Juma'a 31 ga watan Mayun 2019.

Marigayin wanda ya zama shugaban kungiyar a 2014 ya rasu ne bayan ya yi fama da rashin lafiya.

Yanzu Yanzu: Shugaban PENGASSAN na kasa ya mutu

Yanzu Yanzu: Shugaban PENGASSAN na kasa ya mutu
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Diyar Atiku ta ce ba za ta taba mantawa da mulkin APC ba

Sakataren kungiyar PENGASSAN, Okugbawa Lumumba ne ya tabbatar da rasuwar John a hirar wayar tarho da ya yi da majiyar Legit.ng.

Lumumba ya ce mambobin kungiyar suna kan hanyar zuwa gidan marigayin domin jajanta musu kuma ya ce kungiyar za ta fitar da sanarwa na musamman nan gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel