Kasafin kudin 2019: Buhari zai kashe N1bn a tafiye-tafiye

Kasafin kudin 2019: Buhari zai kashe N1bn a tafiye-tafiye

Bayanan kasafin kudin 2019, wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu a farkon makon nan, ya nuna cewa shugaban kasar zai kashe zai kashe naira biliyan 1.001 a tafiye-tafiyen gida da waje.

A cewar kasafin kudin, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo har ila yau zai kashe naira miliyan 217.060 a tafiye tafiye na waje da kuma naira miliyan 83. 74 million akan tafiye-tafiyen gida.

An ware naira biliyan 3.822 don kula da kayan wuta da duk wata na’ura a fadar shugaban kasa.

A cewar kasafin kudin, an ware naira miliyan 576. 747 don canja motoci, kayayyakin motoci da tayoyin motocin tawagar tsaro da yan sanda da kuma motocin ayyuka a fadar shugaban kasa.

An ware naira miliyan 395. 834 don gina asibitin fadar shugaban kasa, sannan naira miliyan 395. 834 za ayi amfani dasu wajen gine ginen ofisoshi.

Kasafin kudin 2019: Buhari zai kashe N1bn a tafiye-tafiye

Kasafin kudin 2019: Buhari zai kashe N1bn a tafiye-tafiye
Source: Depositphotos

Shugaban kasar zai kashe naira miliyan 164. 176 akan ayyukan kwararru da alawus na zama, sannan naira miliyan 25 .652 akan kayan abinci da liyafa.

Ofishin shugaban tsaron fadar shugaban kasa ya samu naira miliyan 433. 457 don siyan motocin tsaro da na ayyuka.

Cibiyar lafiya na fadar shugaban kasa ta samu jimlan naira miliyan 798.856, an ware naira miliyan 208. 350 don siyan magunguna sannan naira miliyan 244.364 don siyan kayan gudanar da ayyuka a asibitin.

KU KARANTA KUMA: Osinbajo ya jinjinawa limamin da ya ceci rayukan Kiristoci 300 a masallaci

Sabonta filin kiwon dabbobi tare da gina muhalli da kuma kiyaye kiwon lafiyar namun daji zai dauki naira miliyan 27. 463; sannan gyaran inda ake kebe dabbobi da kuma siyan kayayyakin gwaje gwajen dabbobi a naira miliyan 11. 865.

A halin da ake ciki, za a kashe N8,580,741 wajen siyan takardu a ofishin shugaban kasa a 2019. Jaridu kuma zasu dauki N26, 432, 346, yayin da aka ware N3, 511,909 na mujalla da sauransu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel