Osinbajo ya jinjinawa limamin da ya ceci rayukan Kiristoci 300 a masallaci

Osinbajo ya jinjinawa limamin da ya ceci rayukan Kiristoci 300 a masallaci

Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo a jiya Alhamis, 30 ga watan Mayu ya bayyana limamin addinin Musulunci dan shekara 83, Imam Abdullahi Abubakar, wanda ya ceci Kiristoci 300 daga hallaka a jihar Plateau a matsayin jarumi, wanda ya cancanci karramawa.

Limamin ya cece su ne ta hanyar boye su a cikin masallaci lokacin da wasu yan bindiga suka kai farmaki Yelwan Gindi Akwati, kauyukan Swei da Nghar a karamar hukumar Barkin Ladi da ke jihar Plateau a shekarar da ya gabata.

Osinbajo ya kwararo ruwan yabo ga malamin a fadar Shugaban kasa, Abuja, lokacin da ya karbi bakuncinsa; da na sarkin kauyen Damafulul Mangai, sauran shugabannin garuruwa da wata tawaga da ta hada da yan diflomaasiyya daga Amurka, Ingila da kuma tarayyar turai.

Osinbajo ya karbi bakuncin Imam wanda yak are Kiristoci 300

Osinbajo ya karbi bakuncin Imam wanda yak are Kiristoci 300
Source: Twitter

Da yake bayyana abunda Abubakar yayi a matsayin jarumta, mataimakin Shugaban kasar ya bayyana cewa Imam ya yi namijin kokari domin ya wanzar da zaman lafiya ta hanyar abunda ya aikata fiye da wasu yan siyasa da dama don haka ya cancanci duk wani yabo da karramawa mafi girma.

KU KARANTA KUMA: Ndume ya shawarci Buhari akan abu 1 tal da ya kamata ya mayar da hankali a kai yanzu

Ya bukaci yan siyasa da su guje ma amfani da addini da kabilanci wajen haddasa rabuwar kai a tsakanin mutane.

Yace Imam Abubakar ya nuna wa shugabanni cewa hanyar magance duk wani rikici da ya taso ba wai da rikici bane, sai dai ta hanyar nuna kauna.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel