Rikicin siyasar jihar Kano: An yi mana fashin mulki - Sanata Kwankwaso

Rikicin siyasar jihar Kano: An yi mana fashin mulki - Sanata Kwankwaso

- Kwankwaso ya ce ranar 29 ga watan Mayu ranar bakin ciki ce a garesu

- Ya bayyana cewa rana ce da aka yi musu fashin mulki a kasar nan

- Ya ce bai yi farin cikin rantsar da gwamnoni 29 da aka yi ba a kasar nan

Tsohon gwamnan jihar Kano, kuma Sanatan Kano ta tsakiya, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana cewar ba su murna da rantsar da gwamnoni guda 29 da aka yi ranar 29 ga watan Mayu, inda ya bayar da dalilin sa na cewa "an yi musu fashin mulki ne".

Ya bayyana cewa ranar 29 ga watan Mayu a jihar Kano, ranar bakin ciki ce a garesu.

Tsohon gwamnan ya kara da cewa abubuwan da suka faru ranar 21 ga watan Maris da aka yi zaben gwamnan jihar Kano har gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya samu nasara ya zo musu a ba-zata ne.

Rikicin siyasar jihar Kano: An yi mana fashin mulki - Sanata Kwankwaso

Rikicin siyasar jihar Kano: An yi mana fashin mulki - Sanata Kwankwaso
Source: Twitter

Zaben gwamnan jihar Kano dai ya zo da matsala, inda ya ja hankalin al'umma da dama, bayan an sanar da cewa zaben ba zai kammalu a ranar 9 ga watan Fabrairu ba, inda aka daga zaben zuwa ranar 29 ga watan Maris.

A zaben karon farkon da aka yi ranar 9 ga watan Fabrairu jam'iyyar PDP ce a kan gaba inda ta yiwa jam'iyyar APC tazarar kuri'u sama da dubu 26.

KU KARANTA: Labari mai dadi ga 'yan arewa: Za a fara hako man fetur a jihar Kebbi - Bagudu

An sake maimaita zaben ne a wasu mazabu na kananan hukumomi 28 a fadin jihar ta Kano.

Bayan kammala zaben a karo na biyu jam'iyyar APC ta lashe zaben a mazabun kananan hukumomi 27, inda jam'iyyar PDP ta lashe zaben karamar hukumar Dala kawai.

Siyasar jihar Kano dai ta dauki wani salo tun lokacin da aka sake maimaits zabe a jihar aka bayyana gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda ya lashe zabe.

Da yawa daga cikin mutane musamman a jihar Kano suna ganin cewa magudi kawai jam'iyyar APC ta yi a jihar.

Har yanzu dai mutane basu dai na tofa albarkacin bakinsu akan zaben jihar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel