Labari mai dadi ga 'yan arewa: Za a fara hako man fetur a jihar Kebbi - Bagudu

Labari mai dadi ga 'yan arewa: Za a fara hako man fetur a jihar Kebbi - Bagudu

- Gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Atiku Bagudu ya bayyana cewa za a fara hako danyen man fetur a jihar nan ba da jimawa ba

- Gwamnan ya ce sun samu hadin gwiwar wani kamfani a kasar Jamus domin fara gabatar da aikin

Gwamnatin jihar Kebbi karkashin jagorancin gwamnan jihar Abubakar Atiku Bagudu, ta ce nan ba da dadewa ba jihar za ta shiga jerin jihohin da ake hako danyen man fetur a Najeriya, inda za shiga jerin jihohin da ake hako man fetur ta hanyar hadin gwiwa tsakanin hukumar kula da albarkatun man fetur ta kasa NNPC da kuma gwamnatin jihar.

Labari mai dadi ga 'yan arewa: Za a fara hako man fetur a jihar Kebbi - Bagudu

Labari mai dadi ga 'yan arewa: Za a fara hako man fetur a jihar Kebbi - Bagudu
Source: Depositphotos

Gwamnan ya kara da cewa, "Yanzu haka mun hada kai da wani babban kamfani na kasar Jamus domin samar da abubuwa na more rayuwa. Hakazalika kwanan zamu kaddamar da kamfanin sarrafa tumatiri da kamfanin sarrafa shinkafa ta gida a jihar kamar irin su: WACOT, LABANA da Dangote, kuma yanzu haka manyan kamfanonin da ke garuruwan Yauri da Kamba, suna nan suna cigaba da rubanya abubuwan da suke sarrafawa a kullum," in ji Gwamnan.

KU KARANTA: Takarar shugaban kasa a 2023: Ameachi ya caccaki Peter Obi

Yankin arewacin Najeriya dai shi ma yanzu ya shiga cikin jerin yankunan da ake samar da danyen man fetur a nahiyar Afirka, inda yanzu haka ake hako danyen man fetur a wani bangare na jihar Borno da kuma jihar Bauchi.

Shigar jihar Kebbin cikin jerin jihohin da za a dinga hakar danyen man ba karamin tasiri zai yi wurin bunkasa tattalin arzikin yankin arewacin Najeriyar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel