Lalong zai bayyana manufofinsa na wa’adi na biyu ranar 12 ga Yuni

Lalong zai bayyana manufofinsa na wa’adi na biyu ranar 12 ga Yuni

-Gwamnan Filato ya yi tsokaci kan yadda za'ayi bikin 12 ga watan Yuni a jiharsa.

-A cewarsa a ranar ne zai bayyana kudurorinsa da yake son aiwatarwa a wannan wa'adin nasa na biyu kan mulkin jihar ta Filato.

Gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalong ya ce zai bayyana tsare-tsarensa na wa’adi na biyu a ranar 12 ga watan Yuni yayin ganawa ta musamman da masu ruwa da tsaki a jihar.

Lalong ya yi wannan furcin ranar Laraba bayan an rantsar dashi domin kama aiki a karonsa na biyu a filin kwallon kafar Rwang Pam. Ya ce gwamnatin jiharsa za tayi bikin 12 ga Yuni na ranar dimokuradiyya ta wata muhimmiyar hanya.

Lalong zai bayyana manufofinsa na wa’adi na biyu ranar 12 ga Yuni

Lalong zai bayyana manufofinsa na wa’adi na biyu ranar 12 ga Yuni
Source: UGC

KU KARANTA:Majalisar dattawa za tayi zaman bankwana ranar 6 ga watan Yuni

“ A wannan ranar ne zan bayyana tsare-tsare da nake da su domin wannan zangon na biyu wanda zai kama daga 2019 zuwa 2023 ta hanyar wata ganawa ta musamman. Bayan ganawar zamu tattauna kan dimokuradiyyar Filato daga 2015 zuwa 2019 da kuma abinda muke hari nan da shekaru hudu ma su zuwa.” Inji gwamnan.

Gwamnan ya sake cewa, gwamnatinsa za ta cigaba da bada karfi wurin samar da cigaba ga jama’arta kamar yadda ta fara a wa’adin farko, duk da cewa akwai karancin kudaden aiki.

“ Zai kyautu idan har za muyi waiwaye domin dinke inda muka samu baraka a baya. Hakan shi zai bamu damar yin aikin da zai amfani mutanenmu kana kuma jama’a suyi farin ciki da ayyukan namu.” A cewarsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel