Bikin 12 ga watan Yuni ya fi daraja fiye da na 29 ga watan Mayu – Buhari

Bikin 12 ga watan Yuni ya fi daraja fiye da na 29 ga watan Mayu – Buhari

-Ranar 12 ga watan Yuni ita ce ranar bikin dimokuradiyya a Najeriya yanzu inji fadar shugaban Najeriya.

-Yayin da masu kace nace ke cigaba da magana a kan rashin armashin rantsar da Buhari a ranar 29 ga watan Mayu, Mallam Garba Shehu yayi karin haske a kan lamarin.

Fadar shugaban kasa tayi fatali da ce-ce kucen da ake yi a kan rashin armashin bikin rantsar da Buhari a wa’adin mulkinsa na biyu da akayi ranar 29 ga watan Mayu.

Buba Galadima, wanda ke kan gaba wurin sukar gwamnatin Buhari, ya ce rashin halartar shugabannin kasashen waje da tsoffin shugabannin Najeriya na nuna sun dawo daga rakiyar gwamnatin Buhari.

Bikin 12 ga watan Yuni ya fi daraja fiye da na 29 ga watan Mayu –Buhari

Bikin 12 ga watan Yuni ya fi daraja fiye da na 29 ga watan Mayu –Buhari
Source: UGC

KU KARANTA:Shin ko me ya hana tsoffin shugabannin Najeriya zuwa wajen rantsar da Buhari?

Amma a nasa martanin akan wannan batun, babban mai baiwa shugaban kasar shawara kan harkokin watsa labarai, Mallam Garba Shehu ya shaidawa BBC cewa karya ce kawai da hassada ta wasu mutane.

“ Idan mutane sun girma shekaru sun kama su, yakamata su daina karya saboda za su koma zuwa ga Ubangiji,” inji shi.

Garba Shehu ya ce kasashe 91 suka nuna sha’awar halartar bikin rantsar da Buhari, kuma yawancinsu shugabannin kasashe ne da firaminista.

Ya ce ministocin harkokin waje ne mafi kankantar bakin da suke tunanin halartar bikin. “Biki ne mai farin jini da mutane suke son su zo saboda kima da martabar Buhari.”

Fadar shugaban kasa ta ce an aikawa da shugabannin kasashen waje cewa sai ranar 12 ga watan Yuni za ayi babban bikin ranar dimokuradiyya a Najeriya.

Gwamnatin Buhari ta ce doka ce ta shar’anta a yi ranstuwa ranar 29 ga watan Mayu, amma bikin ranar dimokuradiyya sai ranar 12 ga watan Yuni za ayi shi.

Ana danganta wannan matakin da siyasa, domin farantawa wasu rai da suka dade suna bikin ranar dimokuradiyya a ranar 12 ga watan Yuni.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel