Tambuwal ya rattaba hannu kan wasu sabbin dokoki 4

Tambuwal ya rattaba hannu kan wasu sabbin dokoki 4

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sokoto ya rattaba hannu kan wasu kudirorin dokoki guda hudu.

Kudirorin kun hada da Dokar kafa Asibitin Koyarwa na Murtala Mohammed da Cibiyar Lafiya Bai Daya na shekarar 2019.

Sauran sun hada da na kafa Kwallejin Horas da Ma'aikatan Jinya a Asibiti da Cibiyar Kulawa da Harkokin Kiwon Lafiya na JIhar Sokoto na shekarar 2019.

Tambuwal ya rattaba hannu kan wasu kudirorin dokoki guda 4

Tambuwal ya rattaba hannu kan wasu kudirorin dokoki guda 4
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Masana sun bayyana kudin sabuwar motar shugaba Buhari

Sanawar da ta fito daga Dirkta Janar na Yadda labarai da Hulda da Jama'a na gwamnan, Abubakar Shekara ta ce sabbin dokokin za su taimaka wurin kawo cigaba a fanin kiwon lafiya a jihar.

"A baya, gwamnatin Tambuwal ta bayyana niyyar ta na kafa asibitin koyarwa a jihar ta yiwa wasu dokoki garambawul domin inganta fanin kiwon lafiya a jihar," inji shi.

Ya kara bayanin cewa dokar Asibitin Koyarwa na Murtala Mohammed zai bayar da damar kafa kwamitin direktoci da babban direktan harkokin kiwon lafiya daga hukumomin masu alaka da kiwon lafiya domin tafiyar da harkokin asibitin.

Ya kara da cewa Kwallejin Nazarin Aikin Jinya zai rika koyar da kwasa-kwasai da na Satifiket, Diploma da Digiri tare da bayar da damar gudanar da bincike kan Kimiyyar Aikin Jinya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel