Sojoji sun kai samame ofishin Hisbah don kwatar kwalaben giya a Jigawa

Sojoji sun kai samame ofishin Hisbah don kwatar kwalaben giya a Jigawa

Wasu dakarun rundunar Sojan kasa sun kai samame babban ofishin hukumar Hisbah ta jahar Jigawa dake garin Dutse da nufin kwato wasu dimbin kwalaben giya da jami’an hukumar suka kwace a wasu gidajen shan barasa dake garin Dutse.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito babban kwamandan Hisbah na jahar Jigawa, Malam Ibrahim Dahiru Garki ne ya sanar da haka a ranar Alhamis, 30 ga watan Mayu a garin Dutse, inda yace jami’an Hisbah sun dakile yunkurin Sojojin.

KU KARANTA: Sabon gwamna ya kara mata ta 3 kwana daya bayan darewarsa madafan iko

Garki yace da sanyin safiyar Laraba, 29 ga watan Mayu ne jami’an Hisbah suka bi wasu gidajen shan barasa dake garin Dutse, inda suka kwace kwalaben haramtattun giya har katan 70, sai gashi da misalin karfe 4 na ranar wasu Sojoji su 7 suka dira ofishin Hisban da nufin kwace kwalaben giyan da karfi da yaji.

Malam Garki yace samun labarin hakan keda yayi gaggawar tuntubar shugaban hukumar tsaron sirri ta DSS dake Dutse, da kuma kwamishinan Yansandan jahar, wadanda suka aika da jami’ansu zuwa pfishin Hisban, da haka Sojojin suka juya ba tare da daukan komai ba.

Da majiyarmu ta tuntubi kwamandan Operation Salama dake garin Dutse, 2nd Laftanar M.I Ikemba game da batun, sai yace sharri ake ma dakarun Soja, a cewarsa babu wani ko wasu Sojoji suka shiga ofishin Hisbah da nufin kwatan kwalaben giya.

Shima kwamishinan Yansandan jahar, Bala Zama Sanchi ya bayyana cewa Sojojin basu shiga ofishin Hisbah ba, kawai dai suna aikin sintiri ne a yankin, amma basu taba kowa ba, kuma basu dauki komai ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel