EFCC ta kammala shirin gurfanar da ma'aikaciyar JAMB da ta ce maciji ya hadiye N35m

EFCC ta kammala shirin gurfanar da ma'aikaciyar JAMB da ta ce maciji ya hadiye N35m

A ranar juma'a 31 ga watan Mayu, hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) zata gurfanar da ma'aikaciyar hukumar JAMB, Philomina Chishe, tare da wasu ragowar mutane biyar a kan badakalar miliyan N35.

Rahotanni sun bayyana cewar Chishe ta sanar da hukumar EFCC cewar maciji ne ya hadiye kudin da ake zarginsu da wawure wa, kamar yadda jaridar 'The Nation' ta wallafa.

Ragowar mutane biyar da za a gurfanar tare da Chishe sune; Samuel Umoru, Yakubu Jekada, Daniel Agbo, Priscilla Ogunsola da Aliyu Yakubu. Za a gurfanar da su a gaban babbar kotun tarayya, karkashin mai shari'a jastis Peter Afen, a Abuja.

EFCC ta kammala shirin gurfanar da ma'aikaciyar JAMB da ta ce maciji ya hadiye N35m

Shugaban hukumar EFCC; Ibrahim Magu
Source: Depositphotos

Wani bangare daga cikin takardar shigar da karar ya bayyana cewar; "Philomena, wacce ta kasance ma'aikaciyar hukumar JAMB a jihar Benuwe, tayi suna a fadin Najeriya bayan tayi wani kalami mai ban mamaki a kan cewar wani shu'umin maciji ne ya hadiye miliyan N35 da hukumar ta tattara daga sayar da katin rijista a jihar."

DUBA WANNAN: Sabon gwamnan Zamfara ya sadaukar da albashinsa ga gidan marayu

A binciken kwakwaf da ta gudanar, EFCC ta ce ta gano cewar an samu gibin biliyan N8.7 a kudaden da JAMB ta tattara daga sayar da katin rijista.

Wasu jami'an 'yan sanda sun taba bayyana cewar beraye sun cinye kullin tabar wiwi fiye da 100 da suka ajiye a ofishinsu a matsayin shaida bayan sun kama dila dake sayar da ita ga jama'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel