Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane 2 a Katsina

Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane 2 a Katsina

Rundunar yan sanda sun yi nasarar kasha wasu masu garkuwa da mutane biyu bayan wani mamaya da suka kai kan daya daga cikin sansaninsu da ke kauyen Illela da ke karamar hukumar Safana a jihar Katsina.

Kwamishinan yan sandan jihar Katsina, Sanusi Buba ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 30 gwatan Mayu.

Da yake jawabi a yau Alhamis a wani zantawa, CP Buba yace da misalin awa 13, jami’an atisayen Operation Puff Adder sun kai farmaki sansanin sannan suka yi arangama da yan ta’addan, inda suka yi musayar wuta.

Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane 2 a Katsina

Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane 2 a Katsina
Source: Depositphotos

A cewarsa, tawagar sun yi nasarar fatattakan yan iskan daga mafakarsu sakamakon haka ne mutum biyu daga cikin yan bindigan suke mutu a lokan arangaman.

“Sauran sun tsere zuwa daji. Tawagar ta samo bindigar AK 47 guda daya mai lamba 1986RG8604 da Babura hudu,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Kotun daukaka kara ta yi wancakali da hukuncin da ya soke cancantar takarar Ademola Adekele

Ya kara da cewa: “An kuma kama daya daga cikinsu da ransa sannan za mu yi duk abunda ya kamata, domin mu ajiye shi da ransa domin samun bayanai masu inganci yayinda muke ci gaba da yaki da yan bindiga."

A baya Legit.ng ta rahoto cewa dan takarar kujerar shugaban majalisar dattawa, Sanata Muhammadu Ali Ndume, ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dakatar da komai a halin yanzu sannan ya mayar da hankali ga lamarin tsaro a kasar.

Yayin da yake hira da manema labarai a ranar Alhamis, 30 ga watan Mayu a Maiduguri, Sanata Ndume yayi korafin cewa kusan kowani yanki na kasar nan na fuskntar kalubale akan lamarin tsaro.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel