Ndume ya shawarci Buhari akan abu 1 tal da ya kamata ya mayar da hankali a kai yanzu

Ndume ya shawarci Buhari akan abu 1 tal da ya kamata ya mayar da hankali a kai yanzu

Dan takarar kujerar shugaban majalisar dattawa, Sanata Muhammadu Ali Ndume, ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dakatar da komai a halin yanzu sannan ya mayar da hankali ga lamarin tsaro a kasar.

Yayin da yake hira da manema labarai a ranar Alhamis, 30 ga watan Mayu a Maiduguri, Sanata Ndume yayi korafin cewa kusan kowani yanki na kasar nan na fuskntar kalubale akan lamarin tsaro.

Ndume ya nuna bacin rai game da yanda yan kungiyar Boko Haram ke daukaka ta’addanci, ya roki gwamnati da hukumomin tsaro da su magance lamarin.

Ndume ya shawarci Buhari akan abu 1 tal da ya kamata ya mayar da hankali a kai yanzu

Ndume ya shawarci Buhari akan abu 1 tal da ya kamata ya mayar da hankali a kai yanzu
Source: UGC

“Mun gaji da jin zancen an tsayar da ‘hare-haren yan Boko Haram’ ko an gama da Boko Haram; muna son muji cewar an gama da Boko Haram gaba daya,” cewarsa yayin da yake shawartan gwamnati da hukumomin tsaro da su kafa adadin lokacin da zasu kawo karshen Boko Haram su kuma yi aiki don tabbatar da hakan.

KU KARANTA KUMA: Allah ya raba Buhari da masu jawo masa matsala – Jigon APC ga Buba Galadima

Har ila yau Ndume ya bayyana matukar goyon baya akan kafa yan sandan jihohi don magance rashin tsaro, ya bada shawara ga kowace jiha dake da niyyar yin hakan da su yi koyi da kasashe dake gudanar da irin wannan tsari na aikin yan sanda akan hadin kai da amincewa da dangantaka tsakanin tsare-tsaren yan sandan a tarayya da na jiha.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel