Kungiyar SERAP ta nemi Shugaban Buhari yayi wa tsarin mulki biyayya

Kungiyar SERAP ta nemi Shugaban Buhari yayi wa tsarin mulki biyayya

Kungiyar nan ta “Socio-Economic Rights and Accountability Project” wanda aka fi sani da SERAP ta roki shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya zama mai bin dokokin kasa da tsarin mulki.

Wannan kungiya tayi wannan kira na musamman ga shugaban kasar ne a wata budaddiyar wasika da ta aika masa a Ranar Laraba 29 ga Watan Mayu, ta bakin mataimakin Darektan ta Kolawole Oluwadare.

Mista Kolawole Oluwadare yana so shugaban na Najeriya ya rika bin dokokin kasa; na umarnin kotu da tsarin mulki, sannan kuma ya maida hankali wajen yaki da masu satar dukiyar al’umma a kasar.

“Dole tsarin damukaradiyya ya san da zaman kare hakkin Bil Adama da kuma bin dokokin kasa. Yin watsi da umarnin kotu a lokacin da aka ga dama yana da hadari a yakin da ake yi da rashin gaskiya.”

KU KARANTA: Amaechi yayi wa Peter Obi tas a kan zaben 2023

Mista Oluwadare yake cewa idan gwamnati ta rika bin umarnin kotu, za ta nunawa Duniya cewa babu wanda ya fi karfin iko da umarnin shari’a don haka zai zama tilas kowa ya shiga cikin taitayinsa.

A karshen SERAP ta ke cewa:

“Tsarin mulki da bin umarnin kotu yana cikin manyan ginshikan damukaradiyya, sannan binciken wadanda ake zargi da satar dukiyar gwamnati yana cikin romon mulkin farar hula da cigaban kasa.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel