Kotun daukaka kara ta yi wancakali da hukuncin da ya soke cancantar takarar Ademola Adekele

Kotun daukaka kara ta yi wancakali da hukuncin da ya soke cancantar takarar Ademola Adekele

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta yi wancakali da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke inda ta soke cancantar takarar Ademola Adekele, dan takarar gwamna na PDP a zaben jihar Osun.

Da ta ke zartar da hukunci a yau Alhamis, 30 ga watan Mayu kotun ta ce Kotun Tarayya ta tafka kuskure da ta soke takarar Adeleke, “alhali hujjoji a gaban kotun sun nuna cewa ya cika sharuddan da dokar kasa ta shimfida masa na tsayawa takara.”

Kotun dukaka kara ta ce shaidar da shugaban makarantar da Adeleke ya gabatar game da satifiket na kammala karatun sa, ta wadatar a ce ya cika sharuddan da doka ta shimfida na shiga takarar gwamna.

Kotun daukaka kara ta yi wancakali da hukuncin da ya soke cancantar takarar Ademola Adekele

Kotun daukaka kara ta yi wancakali da hukuncin da ya soke cancantar takarar Ademola Adekele
Source: Depositphotos

Kotun ta ce kotun tarayya ta tafka kuskuren korar Adeleke daga cancantar shiga takara, ba tare da yin la’akari da shaidar da shugaban makarantar da ya kammala ba.

KU KARANTA KUMA: Allah ya raba Buhari da masu jawo masa matsala – Jigon APC ga Buba Galadima

Har ila yau, Kotun daukaka kara ta ce tun farko ma kotun Tarayya ba ta da hurumin da za ta saurari karar, tunda batun da ake magana abu ne da ya shafi jihar Osun.

A yanzu dai a wata shari’ar kuma, Adeleke na kalubalantar nasara da APC ta yi a zaben gwamnan jihar. Shari’ar na a gaban alkalan kotun koli.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Online view pixel