Mun murkushe kungiyar Boko Haram, ba zata kara dawowa ba - Buratai

Mun murkushe kungiyar Boko Haram, ba zata kara dawowa ba - Buratai

- Shugaban rundunar sojojin kasa, laftanal janar Tukur Yusuf Buratai, ya ce tuni dakarun soji suka gama murkushe kungiyar Boko Haram

- Ya bayyana cewar abinda yanzu ke faruwa a yankin arewa maso gabas, aiyukan ta'addanci ne na kungiyar ISWAP

- Ya bayar da tabbacin cewar dakarun soji zasu cigaba da farautar mambobin kungiyar kamar yadda suka yiwa mambobin kungiyar Boko Haram

Shugaban rundunar sojojin kasa, laftanal janar Tukur Yusuf Buratai, ya ce tuni dakarun soji suka gama murkushe kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabas tare da bayyana cewar kungiyar 'yan ta'adda ta IS reshen kasashen Afrika na yamma (ISWAP) ce ke cigaba da kai hare-haren ta'addanci a yankin.

Ya bayyana cewar abinda ake ganin yanzu na faruwa a yankin arewa maso gabas, aiyukan kungiyar ISWAP ce dake samun goyon bayan kungiyar ta'addanci ta IS mai rassa a kasashen duniya. Ya kara da cewa kungiyar na son yin amfani da matsalar tsaron da aka samu a arewacin Najeriya da sauran makwabatan kasasashe domin cigaba da tafka aiyukan ta'addanci.

Buratai ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin Dakta Abubakar Sani, mawallafin littafin 'The Legend of Buratai', wanda ya ziyarce shi a ofis tare da wasu daliban makarantun sakandire 7 dake Abuja.

Mun murkushe kungiyar Boko Haram, ba zata kara dawowa ba - Buratai

Buratai
Source: Twitter

An yi bikin kaddamar da littafin ga jama'a a ranar 17 ga watan Mayu a Abuja, a daidai lokacin da Buratai ke can yankin arewa maso gabas yana gudanar da wata ziyara ga rundunonin soji dake aikin tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Buratai ya bayar da tabbacin cewar dakarun soji zasu yi farautar mambobin kungiyar sannan su murkushe ta kamar yadda suka yiwa kungiyar Boko Haram.

DUBA WANNAN: Buratai ya fadi irin halayen shugabannin da Najeriya ke bukata

Ya kara da cewa duk da Allah ya albarkaci Najeriya da arzikin jama'a da ma'adanai, kasar na bukatar shugabanni masu karfin hali da juriya da sadaukar wa kafin ta iya ganin bayan kalubalen da take fuskanta.

Kazalika ya nuna jin dadinsa bisa yadda Dakta Sani ya rubuta littafi a kan irin gudunmawar da ya bawa kasa, musamman a bangaren tsaro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel