Allah ya raba Buhari da masu jawo masa matsala – Jigon APC ga Buba Galadima

Allah ya raba Buhari da masu jawo masa matsala – Jigon APC ga Buba Galadima

Wani jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma mai kula da walwalar jam’iyyar na kasa, Ibrahim Masari ya roki Allah da ya kare Buhari daga duk wani mutum da zai janyo masa matsala ko da kuma ‘ya’yan cikinsa ne da ya haifa.

Masari yabayyana hakan ne yayinda yake mayar da martani ga tsohon makusancin Buhari kuma jigo a yakin neman zaben Atiku Abubakar a 2019, Buba Galadima.

Buba Galadima dai ya yi ikiran cewa ya fi wa talakawan Najeriya amfani fiye da gwamnatin Buhari.

Allah ya raba Buhari da masu jawo masa matsala – Jigon APC ga Buba Galadima

Allah ya raba Buhari da masu jawo masa matsala – Jigon APC ga Buba Galadima
Source: Facebook

Masari yace: “A iya sanina na san cewa duk abin da kake yi don Allah, to Allah zai taimake ka. Kila Buba Galadima Allah ya duba zuciyarsa sai ya ga cewa ba don Allah yake bin Muhammadu Buhari ba, bad a zuciya daya yake bin sa ba.

“Idan za ka tuna duka takarkarin da Buhari ya yi a baya da aka samu akasi, su Buba suke shige gidan gaba suna yin abin da suka ga dama.

KU KARANTA KUMA: Yadda wani Fasto ya yiwa mata 20 ciki a cocinsa

“Kamar yadda ake raba gyada haka Buba Galadima ke raba takara, ya soke wannan ya ba da wannan. Ina ganin haka a matsayina na dan siyasa mai fahimta, yadda ake tafiyar da al’amurran siyasa, shi yasa nake ganin aka yi ta samun matsala.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel