Fusatattun 'yan takara 5 na APC sun nemi a cire sabon gwamnan Borno

Fusatattun 'yan takara 5 na APC sun nemi a cire sabon gwamnan Borno

- Yan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) 5 a Borno sun bukaci a tsige gwamnan JIhar, Babagana Zulum

- A baya wata kotun tarayya a jihar ta yi watsi da karar da aka shigar na kallubalantar nasarar Zullum bisa dalilin rashin shigar da karar cikin wa'addin kwanaki 14 da doka ta tanada

- Daga baya 'yan takarar sun bukari wata kotun daukaka kara da ke Jos ta warware hukuncin da karamar kotun ta yanke

'Yan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) biyar a Borno sun kallubalancin nasarar zababen gwaman jihar, Babagana Zullum a cikin wata kara da suka shigar a kotun daukaka kara da ke Jos.

Kamfanin dillancin labarai (NAN) ta ruwaito cewa Kotun Tarayya da ke Borno tayi watsi da karar da suka shigar na kallubalantar Zullum bisa dalilin rashin shigar da karar cikin wa'addin kwanaki 14 kamar yadda sashi na 87 na dokar zabe ta tanada.

Fusatattun 'yan takara 5 na APC sun nemi a cire sabon gwamnan Borno

Fusatattun 'yan takara 5 na APC sun nemi a cire sabon gwamnan Borno
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Masana sun bayyana kudin sabuwar motar shugaba Buhari

Sai dai 'yan takarar Mustapha Baba-Shehuri, Kashim Imam, Mohammed Abba-Liman, Mohammed Kumalia da Baba Jatau-Mohammed ba su gamsu da hukuncin kotun ba hakan ya sa suka daukaka kara a kotun daukaka karar.

'Yan takarar ta bakin lauyansu, Obuju Onojah sun bukaci kotun daukaka karar ta soke hukuncin karamar kotun ta kuma soke zaben da akayi yiwa gwamnan kana da umurci jam'iyyar tayi abinda doka ta tanada.

A bangarensa, lauya mai kare wadanda akayi kara, Yusuf Ali ya ki amincewa da daukaka karar inda ya ce ba za tayi tasiri ba duba da yadda karamar kotun tayi watsi da karar na kallubalantar jam'iyyar APC kan wa'adin kwanaki 14.

A jawabin da ya yi, lauyan INEC Usman Tatama shima ya nemi kotun tayi watsi da karar saboda rashin ingancin dalilan.

Bayan sauraron dukkan bangarorin, Mai shari'a U. Onyemenam da ke jagorantar sauran alkalan ya dage yanke hukunci a kan karar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel