Jihar Borno: Yan takaran gwamna 5 sun kai sabon gwamnan kotu

Jihar Borno: Yan takaran gwamna 5 sun kai sabon gwamnan kotu

Mutane biyar da sukayi takaran kujerar gwamnan jihar Borno karkashin jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a ranar Alhamis suna kalubalantan nasarar sabon gwamnan jihar, Babagana Umara Zulun, inda suka kai shi kara kotu.

Yan siyasan biyar sun shigar da kara ne kotun daukaka karan garin Jos, jihar Plateau.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ta bada rahoton cewa babbar kotun jihar Borno ta yi watsi da karar da suka shigar da farko saboda sun shigar da karan bayan kwanaki 14 da dokar zaben Najeriya ya tanada.

Amma yan takaran, Mustapha Baba-Shehuri, Kashim Imam, Mohammed Abba-Liman, Mohammed Kumalia and Baba Jatau-Mohammed, sun nuna rashin amincewasu da hukunicn kotun kuma saboda haka, sun daukaka kara.

KU KARANTA: Karya ne, bamu kama Okorocha da uwargidarsa ba - EFCC

Yan takaran ta bakin kauyansu, Obuju Onojah, ya bukaci kotun daukaka karan ta yi watsi da hukuncin babban kotun tarayya, sannan ta yi watsi da zaben sabon gwamnan sannan a umurci jam'iyyar tayi abinda ya kamata bis aga doka.

Daga cikin wadanda aka shigar kara sune jam'iyyar APC, INEC, da Baba Ahmed Jaddah.

A bangaren lauyan Babagana Zulum, Yusuf Ali, ya nuna rashin yardarsa ga wannan kara da aka shigar saboda babu wani gaskiya cikin lamarin tunda sun gaza bin ka'idar kwanaki 14 kafin shigar da karan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel