Da duminsa: Karya ne, bamu kama Okorocha da uwargidarsa ba - EFCC

Da duminsa: Karya ne, bamu kama Okorocha da uwargidarsa ba - EFCC

- Da yammacin Alhamis, rahotanni sun bazu cewa EFCC ta damke tsohon gwamna jihar Imo

- Kwana daya kenan da saukarsa daga mulkin jihar Imo

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta karyata rahoton cewa ta damke tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha.

Rahotanni sun gabata cewa Jami'an hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arzikin kasa (EFCC) sun dira a Ogboko tare da kama tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, matar sa, Nkechi Okorocha, 'ya'yansa; Gerald Okorocha da Okey Okorocha.

Kazalika cewa hukumar ta garkame jami'ar sa mai suna 'Eastern University' dake garin Ogboko. Tun kafin ya mika mulki, gwamna Rochas ya dade yana korafin cewar hukumar EFCC na gudanar da bincike a kansa tare da shirya yadda zasu kama shi da zarar ya mika mulki.

Amma Kakakin hukumar yaki da rashawan, Tony Oriade, a wata hira da yayi da jaridar Guardian, ya siffanta labarin matsayin bogi.

KU KARANTA: Tsohon ministan Buhari ya goyi bayan kira ga shiomhole yayi murabus

A bangare guda, Kimanin sa'o'i 24 da hawa kan ragamar mulki, sabon gwamnan jihar Imo, Emeke Ihediaha, ya fara rusa ginin gunkin hannun da magabacinsa, Owelle Rochas Okorocha, ya gina a cikin babbar birnin jihar, Owerri.

An nada Ihedioha matsayin gwamnan jihar Imo na shida a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu, 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel