Tsohon ministan Buhari ya goyi bayan kira ga Oshiomhole yayi murabus

Tsohon ministan Buhari ya goyi bayan kira ga Oshiomhole yayi murabus

Tsohon ministan shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Alhaji Adebayo Shittu ya goyi bayan kira ga murabus din Shugaban APC na kasa, Kwamrad Adams Oshiomhole.

A ranar Talata, 28 ga watan Mayu ne mataimakin Shugaban APC na kasa a yankin arewa, Sanata Lawal Shuaibu ya gabatar da wata wasika a bainar jamaá inda ya rubuta cewa Oshiomhole yayi murabus a matsayin Shugaban jam’iyyar na kasa.

A cewar mataimakin shugaban jam’iyyar, Oshiomhole bai yi kokari kamar yadda aka zata ba, don haka yayi murabus.

Tsohon ministan Buhari ya goyi bayan kira ga shiomhole yayi murabus

Tsohon ministan Buhari ya goyi bayan kira ga shiomhole yayi murabus
Source: UGC

Da yake martani ga wannan kira na Oshiomhole yayi murabus, Shittu yace “Na goyi bayan haka”.

Da yake ci gaba da magana, tsohon ministan sadarwan, wanda Oshiomhole yaki bari yayi takara a matsayin dan takarar gwamnan APC a jihar Oyo yace: “Gaskiya ne idan har Oshiomhole na nan jam’iyyar nan za ta durkushe a da zaran Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gama mulkinsa na biyu.

“Oshiomhole na ji da kansa sannan yana da matsalar son kai kuma yana so ace ya sha kan duk wani wuri kuma ba haka damokradiya take ba. Na san cewa da dama daga cikinmu wadanda suka kasance mambobin jam’iyyar nan ne masu tunanin makomarta a gaba sannan kuma idan har ana so jam’iyyar nan ta ci gaba har baya mulkin Shugaban kasa Muhammadu Buhari toh sai an aiwatar da hakan. Muna duba duk abunda ya kamata muyi domin ingiza shi waje, za mu yi shi.”

KU KARANTA KUMA: Kada ka yake ni ba zan yake ba – Rochas ya gagadi sabon gwamnan Imo

Har ila yau, wasu daga cikin yanwamitin masu ruwa da tsaki da suka nemi a boye sunansu, sunce matsalar Shugaban jam’iyyar shine yana so ace shi yayi komai.

A cewarsu, Oshiomhole ne ke gudanar da kusan komai na ofishin jam’iyyar na kasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel