Buhari ya ki amincewa da wasu sabbin kudurori 2 daga majalisar dattawa

Buhari ya ki amincewa da wasu sabbin kudurori 2 daga majalisar dattawa

Shugaba Muhammadu Buhari ya ki saka hannu a kan kudirin neman kafa Jami'ar Maritime ta Najeriya (NMU) da majalisar tarayya ta aike masa da shi.

Buhari ya kuma ki amincewa da kudirin kafa cibiyar 'institute of chartered biochemist and molecular biologist' na 2019.

Shugaban kasar ya aike wa majalisa sakon sa ne cikin wasu wasiku biyu mabanbanta da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu ya karanto a zauren majalisar a ranar Alhamis.

Buhari ya ki saka hannu a kan dokar neman kirkirar jami'ar Maritime

Buhari ya ki saka hannu a kan dokar neman kirkirar jami'ar Maritime
Source: Twitter

A batun kudin kafa Jami'ar Maritime, Buhari ya ce kudaden da ake bukata wurin kafa jami'ar sunyi yawa sosai.

DUBA WANNAN: Masana sun bayyana kudin sabuwar motar shugaba Buhari

"Kamar yadda ya ke a sashi na 58 (4) na kudin tsarin mulkin kasa na 1999 da aka yiwa kwaskwarima, ina son sanar da majalisar dattawa rashin amincewa ta kan kudirin kafa Maritime University na 2018 da majalisar da amince da shi," inji shi.

"Na ki amincewa da kudirin ne saboda kudaden da ake bukata wurin kafa jami'ar sunyi yawa kuma hakan na iya shafar ayyukan wasu hukumomi da ma'aikatun gwamnati."

A kan kudirin chartered biochemist and molecular biologist bill, Buhari ya ce akwai wata cibiya ta chartered institute biochemist da ke yin da ayyukan da ake neman sabuwar cibiyar da rika gudanarwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel