Buratai ya fadi irin shugabannin da Najeriya ke bukata

Buratai ya fadi irin shugabannin da Najeriya ke bukata

Shugaban rundunar sojojin kasa, laftanal janar Tukur Yusuf Buratai, ya ce Najeriya na matukar bukatar shugabannin masu kishi da kuma riko da gaskiya.

Buratai ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin Dakta Abubakar Sani, mawallafin littafin 'The Legend of Buratai'.

An yi bikin kaddamar da littafin ga jama'a a ranar 17 ga watan Mayu a Abuja, a daidai lokacin da Buratai ke can yankin arewa maso gabas yana gudanar da wata ziyara ga rundunonin soji dake aikin tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Shugaban rundunar sojin ya bayyana cewa 'yan Najeriya da dama sun kafa tarihi a bangarori daban-daban tun bayan samun 'yanci a shekarar 1960.

Ya ce gudunmawar da irin wadannan mutane suka bayar ce ta bawa mutane irinsa kwarin gwuiwar zage dantse wajen hidimtawa kasa.

Buratai ya fadi irin shugabannin da Najeriya ke bukata

Buratai
Source: Depositphotos

Ya kara da cewa duk da Allah ya albarkaci Najeriya da arzikin jama'a da ma'adanai, kasar na bukatar shugabanni masu karfin hali da juriya da sadaukar wa kafin ta iya ganin bayan kalubalen da take fuskanta.

Kazalika ya nuna jin dadinsa bisa yadda Dakta Sani ya rubuta littafi a kan irin gudunmawar da ya bawa kasa, musamman a bangaren tsaro.

DUBA WANNAN: Kwana daya da mika mulki, EFCC tayi awon gaba da tsohon gwamnan APC da matar sa da 'ya'yansa biyu

A nasa jawabin, Dakta Sani ya bayyana cewar ya yanke shawarar rubuta littafi a kan Buratai ne bayan ya sadu da dumbin matasa, dalibai, dake son shiga aikin soja domin su zama jarumai kamar Buratai.

Dakta Sani ya ziyarci Buratai ne tare da wasu dalibai daga makarantun sakandire guda 7 dake Abuja, wanda suka hada da makarantar sakandire ta 'ya'yan sojoji.

Da yake amsa tambayar wata daliba a kan sirrin nasarorin da ya samu, Buratai ya ce hakan ba zai rasa nasaba da nacinsa da dagewa a kan abinda yasa a gaba ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel