Yanzu-yanzu: Sabon gwamna ya fara aiki ta hanyar rushe ginin da magabacinsa yayi

Yanzu-yanzu: Sabon gwamna ya fara aiki ta hanyar rushe ginin da magabacinsa yayi

Kimanin sa'o'i 24 da hawa kan ragamar mulki, sabon gwamnan jihar Imo, Emeke Ihediaha, ya fara rusa ginin gunkin hannun da magabacinsa, Owelle Rochas Okorocha, ya gina a cikin babbar birnin jihar, Owerri.

An nada Ihedioha matsayin gwamnan jihar Imo na shida a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu, 2019.

Ginin 'Akachi Tower' ya kasance daya daga cikin gine-ginen ban sha'awa da tsohon gwamnan yayi amma an waye gari ana ciki rusheshi.

Yanzu-yanzu: Sabon gwamna ya fara aiki ta hanyar rushe ginin da magabacinsa yayi

Yanzu-yanzu: Sabon gwamna ya fara aiki ta hanyar rushe ginin da magabacinsa yayi
Source: Facebook

KU KARANTA: Majalisar dattawa za tayi zaman bankwana ranar 6 ga watan Yuni

Gwamna Rochas Okorocha ya gina wannan abu ne a wuri da ya kasance Bola a baya, amma da alamun yana iya komawa bola kuma.

Sojoji, wadanda suke zagaye da ginin yayi rusashi sun hana yan jarida daukan hoton wannan aiki.

Kimainn mako daya da ya wuce mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya kaddamar da wannan gini.

Ana kyautata zaton bayan rusa wannan gini, sabon gwamnan zai rusa wasu manyan gine-ginen gunkayen shugabannin Afrika da Rocha Okorocha ya gina.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel