Tsohon Ministan Sadarwa ya nemi Oshiomhole ya yi murabus

Tsohon Ministan Sadarwa ya nemi Oshiomhole ya yi murabus

Tsohon Ministan sadarwa na Najeriya, Adebayo Shittu, ya bayyana goyon baya akan kiraye-kirayen ganin shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole ya yi murabus daga kujerar sa ta jagorancin jam'iyya mai ci a kasar nan.

Tsohon ministan wanda jam'iyyar APC bisa jagorancin Kwamared Oshiomhole ta yi fatali da cancantar tsayawar sa takara a zaben fidda gwanin takarar kujerar gwamnan jihar Oyo, ya ya sanya kulla gaba ta takun saka da tsohon gwamnan na jihar Edo.

Tsohon Ministan Sadarwa ya nemi Oshiomhole ya yi murabus

Tsohon Ministan Sadarwa ya nemi Oshiomhole ya yi murabus
Source: UGC

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, tsohon ministan ya bayyana ra'ayin sa ne dangane da wasikar neman sauka daga kujerar jagoranci da mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa, Sanata Lawal Shu'aibu ya aike da ita zuwa Oshiomhole.

Sanata Shu'aibu wanda ya kasance mataimakin shugaban jam'iyyar APC reshen Arewa, ya nemi Oshiomhole da ya yi murabus cikin gaggawa a sakamakon zargin sa da yin kutse wajen sauya wasu hukunce-hukunce da jam'iyyar ta zartar.

KARANTA KUMA: Gwamna Fintiri ya nada sakataren gwamnati a jihar Adamawa

Tsohon Ministan ya kara da cewa, bayan shudewar shugaban kasa Muhammadu Buhari a karshen wa'adin mulkin sa, to kuwa babu makawa jam'iyyar APC za ta durkushe muddin Oshiomhole ya ci gaba da kasancewa akan karaga ta jagorancin ta.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel