Najeriya ta kashe N11trn wurin biyan tallafin man fetur a shekara 6 –inji majalisa

Najeriya ta kashe N11trn wurin biyan tallafin man fetur a shekara 6 –inji majalisa

-Sanata Kabir Marafa ya bayyana adadin kudade da Najeriya ta kashe cikin shekara 6 domin biyan tallafin man fetur.

-Sanatan yayi wannan jawabin ne ranar Alhamis a majalisar dattawa, inda yanzu kuma majalisar ta dage zama har zuwa 6 ga watan Yuni wanda zai kasance zaman bankwana ga majalisa ta 8.

Shugaban kwamitin man fetur na majalisar dattawa Kabir Marafa ne yayi wannan bayani a ranar Alhamis inda yace Najeriya ta kashe kudin da ya kai N11trn cikin shekaru 6 domin biyan tallafin man fetur.

Kazalika, majalisar dattawa ta amince da biyan N129bn a matsayin biyan bashi zuwa ga masu kasuwancin man fetur guda 67.

Najeriya ta kashe N11trn wurin biya tallafin man fetur a shekara 6 –inji kwamitin majalisar dattawa

Najeriya ta kashe N11trn wurin biya tallafin man fetur a shekara 6 –inji kwamitin majalisar dattawa
Source: Twitter

KU KARANTA:Shin ko me ya hana tsoffin shugabannin Najeriya zuwa wajen rantsar da Buhari?

Amincewar dai ta biyo bayan rahoton da kwamitin da shi Marafan ke jagoranta akan wasu tsare-tsare da suka hada da masu kasuwancin man, ya kawo gaban majalisar, wanda ya samu karbuwa ba tare da wata matsala ba.

A karshe, majalisar ta bayyana ranar 6 ga watan Yuni, 2019 a matsayin ranar da za tayi zamanta na karshe wanda ta sanyawa taken zaman bakwana.

A wani labari makamancin wannan, shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa sanata Lawan Ahmad yace masu dukiya sunfi karfin shari'a a Najeriya.

A cewarsa, masu tarin dukiya na iya sayen hukunci da suke so ayi masu a wannan kasa tamu. Sanatan yayi fatan a yanzu za'a samu canjin irin wannan dake aukuwa a kasarmu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel