SEC: Kotu ta bayar da umurnin mayar da Mounir Gwarzo

SEC: Kotu ta bayar da umurnin mayar da Mounir Gwarzo

Kotun ma'aikata da ke Babban Birnin Tarayya Abuja ta bayar da umurnin a mayar da dakataccen shugaban hukumar kula da hada-hadan hannun jari (SEC), Mounir Gwarzo bakin aikinsa ba tare da bata lokaci ba.

Daily Trust ta ruwaito cewa tsohuwar Ministan Kudi, Kemi Adeosun ce ta dakatar da Gwarzo a ranar 29 ga watan Nuwamban 2017 sannan ta kafa kwamitin bincike kan zargin almundahar kudi da ake zarginsa da aikatawa.

Daga bisani Gwarzo ya kallubalanci dakatar da shi da akayi da rahoton da kwamitin binciken da aka kafa ta bayar a kansa.

SEC: Kotu ta bayar mayar da Munnir Gwarzo

SEC: Kotu ta bayar mayar da Munnir Gwarzo
Source: UGC

DUBA WANNAN: Masana sun bayyana kudin sabuwar motar shugaba Buhari

A yayin yanke hukunci a ranar Alhamis, Alkalin kotun, Mai Shari'a Sanusi Kado ya ce tsohuwar ministan kudin ba ta da ikon dakatar da Gwarzo.

Hakan ya sa Kado ya ce dakatarwar ba ta da tasiri.

Alkalin ya kuma ce kwamitin binciken da aka kafa ba kotu ba ce ko wani bangare na fannin shari'a illa kawai kwamiti ne da aka kafa domin yin bincike.

Ya kuma bukaci a ajiye hukuncin kwamitin binciken a gefe guda.

Kazalika, ya bukaci a mayar da Gwarzo kan mukaminsa na Direkta Janar na SEC domin ya karasa wa'adinsa na tsawon shekaru biyar.

Bugu da kari ya ce a biya Gwarzo dukkan albashi da allawus dinsa na tsawon lokacin da suka wuce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel