Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da babban Malami a Katsina

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da babban Malami a Katsina

Gungun yan bindiga sun yi garkuwa da wani malamin kwalejin kimiyya da fasaha ta Hassan Usman dake jahar Katsina, Dakta Bello Birchi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun yi awon gaba da Dakta Bello ne daga gidansa dake kan titin zuwa garin Dutsanma a kauyen Tashar Bara’u cikin karamar hukumar Birchi, a daren Alhamis.

KU KARANTA: Tsohuwa yar shekara 100 ta rasu tare da yayanta 3 bayan sun ci guba a abinci

Shugaban kungiyar Malaman kwalejin kimiyya da fasaha, Dakta Sabi’u Yau Abdullahi ne ya tabbatar da sace abokin aikin nasu, inda yace lamarin ya jefa kafatanin malaman kwalejin cikin halin dimuwa, alhini da jimami.

“Har yanzu masu garkuwan basu tuntubi kowa ba, balle mu san halin da yake ciki.” Inji Dakta Sabi’u Yau Abdullahi.

Kimanin watanni biyu kenan yan bindiga sun tsananta kai hare hare a jahar Katsina, musamman a kananan hukumomin Kankara, Dutsanma da kuma Batsari, da kauyukan dake zagaye dasu.

Ko a ranar 16 ga watan Mayu an samu wasu gungun yan bindiga da yawansu ya kai 20akan babura dauke da bindigu suka kai farmaki kauyukan Dan Marke, Dan Sabau da Karya a karamar hukumar Kankara.

A wannan harin da suka kai, yan bindigan sun kashe akalla mutane 20 da basu ji ba, basu gani ba, kamar yadda shugaban riko na karamar hukumar Kankara ya tabbatar, inda yace dukkanin kauyukan suna makwabtaka da jahar Zamfara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel