Majalisar dattawa za tayi zaman bankwana ranar 6 ga watan Yuni

Majalisar dattawa za tayi zaman bankwana ranar 6 ga watan Yuni

-Majalisar dattawa ta 8 ta sanar da ranar zamanta na karshe wanda zai kama ranar 6 ga watan Yuni, 2019.

-Mataimakin shugaban majalisar, Ike Ekweremadu ne ya bada wannan sanarwa a ranar Alhamis, inda ya roki takwarorinsu da cewa su daure su halarci wannan zama.

Majalisar dattawa zata gudanar da zamanta na karshe wanda shi ne zai kasance na bankwana a ranar 6 ga watan Yunin 2019.

Mataimakin shugaban majalisar Ike Ekweremadu ne yayi wannan sanarwa a ranar Alhamis bayan da majalisar ta kammala zamanta na ranar.

Malisar dattawa za tayi zaman bankwana ranar 6 ga watan Yuni

Malisar dattawa za tayi zaman bankwana ranar 6 ga watan Yuni
Source: Facebook

KU KARANTA:Gwamnoni 12 da suka sauka daga kan kujerar mulki

Ekweremadu yayi kira ga ilahirin sanatocin da suyi kokari su halarci zaman na ranar 6 ga watan Yuni wanda shi ne zai kasance zama na bankwana kuma na karshe ga majalisa ta 8.

Majalisar ta 8 an kaddamar da ita ne a ranar 9 ga watan Yunin 2015, inda ta samu sanata Bukola Saraki da Ike Ekweremadu a matsayin shugaba da mataimakin shugabanta.

A wani labari mai kama da wannan, shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa wato sanata Lawan Ahmad yayi Allah wadai da irin halin bangaren shari'ar kasar nan.

A cewarsa, "duk wani mai dukiya a kasar Najeriya to sayen shari'a yakeyi. Abin nufi sai hukuncin da ya ga dama za'a yanke masa."

Sanatan yayi wannan furucin ne yayinda majalisar dattawa ke kokarin tabbatar da Abubakar Musa Sadik a matsyin shugaban kotun daukaka kara na gargajiya ta Abuja.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel