Gwamna Fintiri ya nada sakataren gwamnati a jihar Adamawa

Gwamna Fintiri ya nada sakataren gwamnati a jihar Adamawa

Sabon gwamnan jihar Adamawa Alhaji Ahmadu Fintiri, ya nada tsohon kwamisha, Injiniya Ahmad Bashir a matsayin sakataren sabuwar gwamnatin sa ta jihar Adamawa.

Fintiri ya nada wani dan jarida, Solomon Kumangar a matsayin daraktan sadarwa na fadar gwamnatin sa. Kazalika ya nada George Kushir, a matsayin babban sakataren yada labarai na mataimakin sa, Sett Crowther.

Gwamnan jihar Adamawa; Ahmadu Fintiri

Gwamnan jihar Adamawa; Ahmadu Fintiri
Source: UGC

Wannan shi ne nadin mukami na farko da sabon gwamna Fintiri ya yi cikin gaggawa bayan karbar rantsuwa ta riko da akalar jagorancin jihar Adamawa da aka gudanar a ranar Laraba, 29 ga watan Mayun 2019.

Sabon sakataren gwamnatin jihar Adamawa, Ahmad Bashir, ya kasance tsohon kwamishinan ayyuka da gidaje yayin da Fintiri ya rike kujerar mukaddashin gwamnan jihar na tsawon watanni uku a shekarar 2014.

KARANTA KUMA: Kotun koli ta yi fatali da zaben sanatan PDP na jihar Delta, Ned Nwoko

Solomon Kumangar, sabon daraktan sadarwa na fadar gwamnatin jihar Adamawa, ya kasance mai watsa labarai a gidan talabijin na ATV, Adamawa Television, yayin da George Kushir ya kasance mai yada labarai a gidan talabijin na AIT reshen birnin Yola.

Yayin rantsar da su cikin fadar gwamnatin sa a ranar Alhamis, gwamna Fintiri ya ce wannan sabon nadi na zuwa ne bayan tabbatar da kwarewar su akan aiki da kuma nagarta ta gaskiya da rikon amana.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel