Daga mika mulki: Jami'an EFCC sun dira gidan tsohon gwamnan APC, sun yi awon gaba da shi da matar sa

Daga mika mulki: Jami'an EFCC sun dira gidan tsohon gwamnan APC, sun yi awon gaba da shi da matar sa

Jami'an hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arzikin kasa (EFCC) sun dira a Ogboko tare da kama tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, matar sa, Nkechi Okorocha, 'ya'yansa; Gerald Okorocha da Okey Okorocha. Kazalika hukumar ta garkame jami'ar sa mai suna 'Eastern University' dake garin Ogboko.

Tun kafin ya mika mulki, gwamna Rochas ya dade yana korafin cewar hukumar EFCC na gudanar da bincike a kansa tare da shirya yadda zasu kama shi da zarar ya mika mulki.

A jiya ne alkalin alkalan jihar Imo, Paschal Nnadi, ya rantsar da sabon zababben gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha, tare da mataimakinsa a filin wasa na Dan Anyiam dake Owerri da misalin karfe 11:00 na rana.

Da yake gabatar da jawabi jim kadan bayan an rantsar da shi, Ihedioha ya bayyana takaicinsa a kan yadda gwamnatin Rochas ta lalata dukkan bangarorin gwamnatin jihar da suka hada da majalisa, lafiya, ilimi da bangaren shari'a.

Daga mika mulki: Jami'an EFCC sun dira gidan tsohon gwamnan APC, sun yi awon gaba da shi da matar sa

Rochas Okorocha
Source: Twitter

Da yake mayar da martani, Mista Sam Onwuemeodo, sakataren yada labaran Rochas ya ce bai yi mamakin kalaman sabon gwamnan ba, tare da bayyana cewar Rochas ya yiwa jihar Imo fiye da abubuwan da ya dauki alkawari.

DUBA WANNAN: Sakkwatawa sun kaurace wa wurin rantsar da Tambuwal a Sokoto (Hotuna)

A cewar Onwuemeodo, daga cikin nasarorin da Rochas ya samu akwai bayar da ilimi kyauta, samar da tsaro da raya karkara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel