Wasa farin girki: Buhari ya amince a biya yan fansho naira bilyan 22.6

Wasa farin girki: Buhari ya amince a biya yan fansho naira bilyan 22.6

Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta amince da biyan yan tsofaffin yan fansho na tsohuwar kamfanin jirgin saman Najeriya, Nigeria Airways, bashin hakkokinsu da suke binta da suka kai naira biliyan 22.4.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito babban sakataren ma’aikatan kudi, Mohammed Dikwa ne ya bayyana haka a ranar Talatar data gabata yayin da yake tattaunawa da manema labaru, inda yace dama can gwamnatin Buhari ta biya kashi 50 na hakkin wasu yan fansho da aka tantance a watan Oktoban shekarar 2018.

KU KARANTA: Tsohuwa yar shekara 100 ta rasu tare da yayanta 3 bayan sun ci guba a abinci

Wasa farin girki: Buhari ya amince a biya yan fansho naira bilyan 22.6

Wasa farin girki: Buhari ya amince a biya yan fansho naira bilyan 22.6
Source: Depositphotos

Sai dai da fari sai da yan fanshon suka tare ma ministan kudi hanya a lokacin da zata fita daga ofishinta a kokarinsu na nuna damuwarsu da rashin amincewarsu game da rashin biyansu hakkokinsu na fansho da suka ce tana kan kan kafa akai.

“An samu tsaiko wajen isar da sakon bayanai tsakanin kungiyan yan fansho da kuma kwamitin tantancewa, yayin da aka shirya gudanar da akin tantancewar daga karfe 10 na safe a kammala karfe 2 na rana, amma ba’a fara ba sai karfe 2 na rana.

“Wannan gibin ne ya kawo matsala, da har wasu yan fanshon suka fara tunanin ba za’a samu tantancesu ba, don haka suka tayar da balli, har ta kaiga sun tare ayarin motocin ministar kudi yayin da zata fice daga ofis.” Inji shi.

Sai dai shima a jawabinsa, shugaban yan fanshon kamfanin jirgin saman Najeriya, San Nzene ya bayyana cewa dalilin tashin hankalinsu shine jami’an da zasu yi aikin tantancewar sunce sun fasa gudanar da aikin saboda suna bin gwamnati bashi, amma gwamnati ta gaa biyansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel