Kada ka yake ni ba zan yake ba – Rochas ya gagadi sabon gwamnan Imo

Kada ka yake ni ba zan yake ba – Rochas ya gagadi sabon gwamnan Imo

Bayan barinsa ofis da kwana daya, tsohon gwamnan jihar Imo, Owelle Rochas Okorocha ya yi gargadin cewa masu neman fadan shi su daina, idan ba so suke ya yake su ba.

A wani faifan bidiyo a kafofin zumunta, an gano inda Okorocha yace, “Yayin da nake barin wannan gida na gwamnatin, kada wanda ya nemi fada na kuma ba zan nemi fadan kowa ba”.

Ya cigaba da yin magana akan cewa kasancewa gwamna kamar sanya rigar “kariya ne”.

Okorocha ya kasance a rigingimun siyasa a lokuta daban-daban, daga jam’iyyansa ta All Progressives Congress, wacce ta dakatar da shi, zuwa hukumar zabe na kasa mai zaman kanta (INEC) wacce ta ki gabatar masa da takardan shaidansa a matsayin wanda ya lashe kujeran sanata a yankin Arewacin Imo.

Kada ka yake ni ba zan yake ba – Rochas ya gagadi sabon gwamnan Imo

Kada ka yake ni ba zan yake ba – Rochas ya gagadi sabon gwamnan Imo
Source: UGC

Haka zalika, sabon gwamnan, Emeka Ihedioha yayi zargin cewa Okorocha ya wulakanta cibiyoyi da dama a jihar a shekaru takwas na gwamnatinsa. Yayi wannan zargin ne yayin da yake yin jawabi a taron bikin rantsar da shi.

KU KARANTA KUMA: Ma’aikatan agaji na ba Boko Haram tallafin kayayyaki - Inji rundunar sojin Najeriya

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Mista Tunji Bello wanda shine sakataren gwamnatin Ambode wato SSG ya yi kaca-kaca da gwamnatin Akinwunmi Ambode inda ya ce a tarihin siyasar Legas ba’a taba samun gwamnati mafi muni kamarta ba.

Bello ya fadi cewa, gwamnatin Ambode bata da kwarewar sanya ayyuka wuraren da yakamata su kasance da kuma tsari na musamman domin cigaban jama’arsu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel