Kotun koli ta yi fatali da zaben sanatan PDP na jihar Delta, Ned Nwoko

Kotun koli ta yi fatali da zaben sanatan PDP na jihar Delta, Ned Nwoko

Reshen kotun kolin Najeriya dake garin Abuja, ya yi fatali da nasarar Ned Nwoko, a matsayin zababben dan majalisar tarayya mai wakilcin shiyyar Delta ta Arewa a majalisar dattawa.

Hukuncin kotun na zuwa ne a ranar Alhamis yayin da ta soke hukuncin wata babbar kotun tarayya da ta umurci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC da ta rataya wa Nwoko nasarar lashe zaben kujerar Sanatan shiyyar Delta ta Arewa.

Ned Nwoko

Ned Nwoko
Source: UGC

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, hukuncin kotun kolin kasar ya bayu a bisa madogara ta sabawa ka'idojin shari'a da babbar kotun tayi yayin zartar da hukunci a bayan karewar wa'adin kwanaki 14 na shigar da korafin.

Ana ci gaba da kirdadon hukuncin kotun kolin ta Najeriya yayin da takaddamar wannan rudani ta auku tun a zaben fidda gwanin takarar kujerar sanatan shiyyar Delta ta Arewa a tsakanin Nwoko da kuma wani dan takara na PDP, Peter Nwaoboshi.

KARANTA KUMA: Masu cancanta kawai zan yiwa nadin mukamai - Masari

A yayin da babbar kotun tarayya ta yi watsi a Nwaoboshi a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar Sanatan ta jihar Delta tare da umurtar hukumar INEC akan tabbatar da nasarar Nwoke, kazalika kotun koli ta warware wannan hukunci.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel