Ma’aikatan agaji na ba Boko Haram tallafin kayayyaki - Inji rundunar sojin Najeriya

Ma’aikatan agaji na ba Boko Haram tallafin kayayyaki - Inji rundunar sojin Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta zargi wasu kungiyoyin Agaji da masu zaman kansu, da ke aiki a yankin Arewa maso Gabas, da yi wa kokarin kakkabe ta’addanci zagon kasa, ta hanyar goyon bayan yan ta’addan Boko Haram.

Kakakin rundunan soji, Sagir Musa, a ranar Alhamis, 30 ga watan Mayu yace rundunar ta gane hakan ne bayan ta kama wani kwamandan Boko Haram, Mohammed Modu a ranar Lahadi.

Rundunar a shekarar 2018 da ya gabata a wani lamari mai kama da haka ta yi zargi akan kungiyoyi masu zaman kansu dake gudanar da ayyuka a yankin.

Mista Musa yayi zargin cewa babban kwamadan ya kasance dan bangaren Abubakar Shekau na kungiyar yan ta’addan.

Ma’aikatan agaji na ba Boko Haram tallafin kayayyaki - Inji rundunar sojin Najeriya

Ma’aikatan agaji na ba Boko Haram tallafin kayayyaki - Inji rundunar sojin Najeriya
Source: Depositphotos

Kakakin sojoji Sagir Musa ya tabbatar da cewa binciken farko da sojoji suka fara yi ya nuna cewa tabbas Boko Haram na bangaren Shekau na “samun agajin abinci da magunguna daga wasu kungiyoyin bada agaji da ke aikin agaji a yankin.”

Sagir ya ce wannan cin amanar kasa ne kuma barazana ce karara ga tsaron kasa.

Mista Musa ya shawarce su dasu gudanar da ayyukansu ba tare da saba ma dokar da aka kafa ba na ma’aikatar ayyukan bada agaji.

Ya kuma bayyana cewa dole aikinsu yayi daidai da tsari da kuma dokar bada agaji na kasa da kasa, har da dokar sasanta rigingimu.

Duk da dai bai bayyana kowace kungiya ba ce, Sagir ya kara da cewa daga yanzu jami’an tsaro ba za su sake sassauta wa wanda duk aka kama da wannan zagon kasa ba.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin PDP na kudu maso gabas da Obiano sun taya Buhari murna

Idan ba a manta ba cikin Disamba 2018, sojoji sun dakatar da ayyukan hukumar UNICEF har sai yadda hali ya yi.

Amma daga baya gwamnatin tarayya ta gaggauta shiga tsakani, aka kashe maganar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel