Allah ne kadai zai iya kiyaye iyakokin Najeriya - Shugabanin tsaro na kasa

Allah ne kadai zai iya kiyaye iyakokin Najeriya - Shugabanin tsaro na kasa

- Shugabanin hukumomin tsaro na Najeriya sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari domin tattaunawa kan kallubalen tsaro da ke adabar kasar

- Shugabanin hukumomin tsaron sun shaidawa shugaban kasa cewa Allah ne kadai zai iya kiyaye iyakokin Najeriya

- Sun kuma shaidawa shugaban kasar cewa yawan shigo da mukamai ta iyakokin Najeriya ne ke hadasa rashin tsaro a kasar

Allah ne kadai zai iya kiyaye mana iyakokin mu - Shugabanin tsaro na kasa

Allah ne kadai zai iya kiyaye mana iyakokin mu - Shugabanin tsaro na kasa
Source: Facebook

Shugabanin hukumomin tsaro a Najeriya sun ce Allah ne kadai zai iya kiyaye iyakokin Najeriya bayan sunyi taro da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A karshen taron da su kayi da shugaban kasar a gidan gwamnati da ke babban birnin tarayya, Abuja, shugabanin hukumomin tsaron sun kuma ce rashin kiyaye iyakokin Najeriya ne dalilin da yasa ake samun karuwar rashin tsaro a kasar.

DUBA WANNAN: Ganduje ya mayar da wasu manyan kusoshin gwamnatinsa kan mukamansu

Shugabanin hukumomin tsaron sun hada da the Shugaban hafsoshin tsaro, Janar Gabriel Olonisakin, shugaban hafsoshin sojoji, Laftanat Janar. Tukur Buratai, Shugaban sojojin ruwa, Rear Admiral Ibok Ekwe Ibas da Shugaban sojojin sama, Air Marshall Abubakar Sadique.

Saura da suka hallarci taron sun hada da mai bawa shugaban kasa shawara a kan tsaro, Babagana Monguno; Ministan Tsaro, Mansur Dan- Ali, Shugaban Hukumar Tattara Bayanan Siiri (NIA), Ahmed Abubakar, Sufeta Janar na 'Yan sanda, Mohammed Adamu da Shugaban Hukumar 'Yan sandan farar Hula (DSS), Yusuf Magaji Bichi.

Shugabanin hukumomin tsaron sun kwashe sama da sa'o'i biyu suna ganawa da shugaban kasan.

Shugaban sojojin ruwa na Najeriya, Rear Admiral Ibok Ekwe da ya yi jawabi a madadin takwarorinsa ya nuna damuwarsa kan yadda makamai barkatai ke shigowa cikin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel