Takarar shugaban kasa a 2023: Ameachi ya caccaki Peter Obi

Takarar shugaban kasa a 2023: Ameachi ya caccaki Peter Obi

- Rotimi Amaechi ya yiwa dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar PDP wankin babban bargo

- Ya ce ya rufewa mutane baki dangane da maganar wanda zai fito takarar shugaban kasa a yankin Igbo

- Ya ce ko zaben da aka gabatar sun gaza samun nasara akan jam'iyyar APC

Ministan tafiye-tafiye, Chibuike Rotimi Ameachi, ya caccaki dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Peter Obi da yace Ameachi ba shi da wani iko a siyasance akan maganar ko kabilar Igbo ne suke da damar fitowa takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

Ameachi wanda yayi jawabi a wurin wani taro da ya halarta a jihar Legas jiya, ya ce tsoho gwamnan jihar Anambra ba shi da ikon yin wata magana akan lamarin saboda ko kujerar shugaban kasa ya kasa sun kasa lashewa.

Takarar shugaban kasa a 2023: Ameachi ya caccaki Peter Obi

Takarar shugaban kasa a 2023: Ameachi ya caccaki Peter Obi
Source: Facebook

Har ila yau Amaechi ya ce tun daga lokacin daga lokacin da ya rike mukamin shugaban majalisar dokokin jihar Rivers zuwa yanzu, sunansa kullum yana shafin farko a cikin jiga-jigan siyasa na kasar nan fiye da Peter Obi.

Amaechi ya bayyana cewa, idan har Igbo suna so su samu kujerar shugaban kasa a 2023 dole ne sai sun shiga an dama dasu a siyasar Najeriya.

KU KARANTA: Cutuka guda 8 da aduwa take maganin su

"Ina goyon bayan shugabancin kasa a gurin Igbo. Na yi imanin cewa Igbo za su fitar da dan takarar shugaban kasa tunda dama can basu taba yi ba. Ba a yiwa Igbo adalci ba idan har ba a barsu sun fitar da dan takara a wannan karon ba. Amma matsalar dole sai kun fito an dama daku tukunna shine zaku samu damar samun kujerar, babu wanda zai zo yace muku lokacin ku yayi ku fito da dan takara. Saboda haka Peter Obi ya rufe mana baki. Ya fadi zabe wanda ni kuma na cinye, kuma har an riga an rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasar Najeriya a karo na biyu," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel