Masu cancanta kawai zan yiwa nadin mukamai - Masari

Masu cancanta kawai zan yiwa nadin mukamai - Masari

A yayin karbar rantsuwa da safiyar ranar Larabar da ta gabata tare da mataimakin sa, Mannir Yakubu, gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya ambato nau'ikan mutane da za su samu shiga cikin sabuwar majalisar gwamnatin sa a karo na biyu.

A ranar Laraba, 29, ga watan Mayun 2019, aka sake rantsar da gwamnan jihar Kastina Aminu Bello Masari tare da mataimakin sa, Mannir Yakubu, a wani sabon wa'adi na riko da akalar jagoranci karo na biyu.

Gwamna Masari yayin da ya kai wa Buhari koken sa na rashin tsaro a jihar Katsina

Gwamna Masari yayin da ya kai wa Buhari koken sa na rashin tsaro a jihar Katsina
Source: UGC

Gwamna Masari tare da mataimakin sa sun karbi rantsuwa a dandalin People Square dake birnin Katsinan Dikko karkashin jagorancin lauyan koli na jihar Katsina, Jastis Musa Danladi.

Cikin jawaban da ya gabatar bayan karbar rantsuwa, Masari ya sha alwashin cewa gwamnatin sa za ta yi nadin mukamai ga mafi kololuwar macancantan mutane da aka tabbatar da nagartar su ta gaskiya da rikon amana.

Ya ce gwamnatin sa za ta yi nadin mukamai da rataya nauyin musamman kan wadanda za su yi tasirin gaske daidai da akidar gwamnatin sa ta inganta jin dadin rayuwar al'umma da kuma kawo ci gaba a jihar ta fannin ingataccen tsaro.

KARANTA KUMA: Ministan Shari'a na Najeriya Abubakar Malami ya yi murabus

A yayin bikin na rantsuwa da aka taikata girman sa domin nuna juyayin salwantar rayukan al'umma da suka afka tarkon ta'addanci musamman a karamar hukumar Batsari, gwamna Masari ya shimfida wasu akidu takwas da gwamnatin sa za ta dabbaka na inganta ci gaba a fannin ilimi, kiwon lafiya, noma, tattalin arziki, da kuma tsayuwa bisa gaskiya da adalci.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel