Babu siyasa cikin soke kwangila da kamfanin Atiku - Shugabar NPA

Babu siyasa cikin soke kwangila da kamfanin Atiku - Shugabar NPA

Shugabar hukumar tashohi jiragen ruwan Najeriya NPA, Hadiza Bala Usman, ta karyata rahoton cewa akwai siyasa cikin soke kwangilar gwamnatin tarayya da kamfanin Intels Nigeria Limited, mallakan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Game da cewar Bala Usman, an soke kwangila da yarjejeniya da kamfanin Intels, mallakan Atiku kan kin tura kudi $145,849,309.33 cikin asusun bai daya gwamnatin tarayya.

A bayanin da Hadiza Bala Usman tayi a wani hirar Rediyo, tace: "Wannan mataki da muka dauka ba siyasa bane. Idan aka fara dabbaka ka'idoji, mutane dole suyi magana. An soke kwangilan ne bayan zabe."

A ranar 29 ga watan Maris, 2019, hukumar NPA ta yanke alakar daukan kaya a jirgin ruwa da yarjejeniya da kanfanin Intels bisa ga sashe na 8, na yarjejeniyar da akayi a ranar 11 ga wtaan Febrairu, 2011.

KU KARANTA: Cutuka guda 8 da aduwa take maganin su

NPA tana tuhumar kamfanin Intels da laifin kin tura kudi dala milyan $145,849,309.33, da suka samu asusun bai daya na gwamnatin tarayya tsakanin 1 ga watan Nuwamba, 2017 da Oktoba 2018.

Amma kamfanin Atiku Intels ta karyata wannan tuhuma inda tace akasin hakan ne saboda ita ke bin NPA bashin $750 million.

Hajiya Hadiza Bala Usman ta yi kira ga gwamnatin jihar Legas da Ogun da su taimaka su samar da filayen da za'a rika ajiye manyan motoci saboda al'ummar jihohinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel