Babu komai tsakani na da Jonathan sai alheri – Inji Gwamna Dickson

Babu komai tsakani na da Jonathan sai alheri – Inji Gwamna Dickson

Gwamna Seriake Dickson na jihar Bayelsa ya bayyana dalilinsa na ba tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan mukami na musamman na jihar da kuma jita-jitar rikicinsa da shugaban.

Seriake Dickson ya bayyana wannan ne a jiya Laraba 29 ga Watan Mayun 2019 lokacin da yake jawabi a gidan rediyo domin fayyace zargin da ake yi na cewa yana rikici da tsohon shugaban.

Gwamna Dickson yake cewa sam babu wani rikici tsakaninsa da Goodluck Jonathan, wanda asalinsa ‘dan jihar Bayelsa ne. Dickson yake cewa akwai kyakkyawar alaka a tsakaninsu.

Mista Dickson yake cewa za a fahimci hakan ne a wajen taron gidauniyar Bayelsa Education Development Fund watau BEDF da aka shirya kwanakin baya a cikin Garin Yenogoa.

KU KARANTA: Daga hawa kan mulki Gwamna ya sallami duka Kwamishinoni

Babu komai tsakani na da Jonathan sai alheri – Inji Gwamna Dickson

Gwamna Dickson ya ba Jonathan mukamin babban mai bada shawara
Source: Depositphotos

A cewar Dickson ya san yadda Jonathan yake da sha’awar ilmi ne tun farko don haka ya ba shi wannan mukami. Gwamnan mai-ci yace wajen Jonathan ya san muhimmancin ilmi a gwamnati.

"Jonathan, babban yaya na ne kuma shugabana, har gobe zan cigaba da ba shi girma, har gobe. Babu dangantakar da ta dade kamar wanda ta ke tsakani na da Jonathan Inji gwamnan."

Seriake Dickson yace: “Wasu ‘yan ka-fi-diri ne kurum ke kokarin kawo matsala tsakanin mu ta hanyar yin wasu baram-barama da kuma kai-komo don kurum ganin kusancin su da tsohon shugaban”

“Duk ranar da na shirya zan je wajen shugaba Jonathan, in zauna kuma in sauraresa. Yana goyon baya na. Muhimmin batun shi ne, ni ne ke rike da jiha kuma akwai wadanda zan zauna domin in karu da su.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel