Shin ko me ya hana tsoffin shugabannin Najeriya zuwa wajen rantsar da Buhari?

Shin ko me ya hana tsoffin shugabannin Najeriya zuwa wajen rantsar da Buhari?

-Wani mai fashin baki akan lamarun siyasa ya ayyana rashin halartar tsoffin shugabannin Najeriya wurin rantsar da Buhari bisa dalilin dangantaka da tayi tsamari a tsakaninsu.

-Dakta Tukur Abdulkadir na jami'ar Kaduna shi ne ya bamu wannan takaitaccen sharhi akan lamarin.

Abubuwa da dama sun auku yayin rantsar da shugaba Muhammdu Buhari a karo na biyu a sararin Eagle square dake Abuja.

Abu na farko dai wanda zai matukar baka mamaki shi ne, idan ka cire Yakubu Gowon babu daya daga cikin tsoffin shugabannin kasar dake raye da ya halarci bikin rantsar da Buhari.

Shin ko me ya hana tsoffin shugabannin Najeriya zuwa rantsar da Buhari?

Shin ko me ya hana tsoffin shugabannin Najeriya zuwa rantsar da Buhari?
Source: UGC

KU KARANTA:Bikin rantsar da gwamnoni : PDP tayi rawar gani ta doke APC inda ta samu kujeru 15 cikin 29

Sai dai kuma a irin wannan ranar a shekarar 2015, kusan za a iya cewa dukkanin tsoffin shugabannin kasar nan sun halarci bikin inda tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya mika mulki ga Buhari.

Masu sharhi kan al’amuran siyasa irinsu Dakta Tukur Abdulkadir na jami’ar Kaduna sun danganta rashin halartar tsoffin shugabannin akan abubuwa guda biyu:

• Raba garin da Buhari ya yi da tsoffin shugabannin

• Kokarin fifita ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar demokradiya ta kasa

Dakta Tukur yace, “ Ina tunanin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo bai halarci taron ba saboda yadda dangantaka ta yi tsamari tsakaninsa da Buhari ta yadda har ana jifar juna da maganganu.”

Shi kuwa shugaba Goodluck Jonathan “Zai yi wuya ya halarci taron kasancewarsa jigo a jam’iyar adawa ta PDP”, inji Dakta Tukur.

To amma Dakta Tukur ya ce yana ganin “rashin halartar tsohon shugaba Abdussalam Abubakar ba ta da nasaba da bacin dangantaka da shugaba Buhari kasancewar shi Abdussalam din yana shiga kusan duk wata sabgar Buhari da aka gayyace shi."

Wani abu dake kara nuna tsamari tsakanin alakar shugaba Buhari da tsoffin shugabannin kasar shi ne a wata hira ta musamman da gidan talabijin na NTA inda Buhari ya furta cewa yana sane da manya kasar nan ba su son sa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel