Tsugune bata kare ba a jihar Kano: An umarci Hakimai 44 na fadin jihar da su hallara a birnin Kano don gabatar da hawan sallah tare da Sarki Sanusi

Tsugune bata kare ba a jihar Kano: An umarci Hakimai 44 na fadin jihar da su hallara a birnin Kano don gabatar da hawan sallah tare da Sarki Sanusi

Tsugune bata kare ba a jihar Kano, yayin da aka umarci dukkanin Hakimai 44 na jihar akan su fara shirin hawan sallah tare da Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II

An umarci dukkanin Hakimai 44 na kananan hukumomin jihar Kano da su fara shirin shigowa birnin Kano, daga ranar Lahadi mai zuwa, Wato ranar 2 ga watan Yunin shekarar 2019, an bukaci Hakiman su hallara ne domin gudanar da bikin hawan sallah karama wanda aka saba gabatarwa duk karshen watan azumin Ramadana, wanda a wannan karon za a gabatar da sallar ranar Talata 4 ga watan Yuni idan Allah ya kai mu.

Tsugune bata kare ba a jihar Kano: An umarci Hakimai 44 na fadin jihar da su hallara a birnin Kano don gabatar da hawan sallah tare da Sarki Sanusi

Tsugune bata kare ba a jihar Kano: An umarci Hakimai 44 na fadin jihar da su hallara a birnin Kano don gabatar da hawan sallah tare da Sarki Sanusi
Source: Twitter

Umarnin ya fito bayan wata takarda da aka aikawa Hakiman wacce aka yi bayani kamar haka:

"Bayan gaisuwa da fatan alheri, ana umartarku daku shigo cikin birnin Kano domin bikin Haye-Hayen Karamar Sallah tare da Dagatan ku da Dawakan ku da Mahayanku a ranar Lahadi 28 ga watan Ramadan Hijira ta 1440 A.H daidai da 2 ga watan Yuni, 2019."

KU KARANTA: Hotuna: Wasu kalaman soyayya da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yiwa matarsa, jim kadan bayan rantsar dasu

"Haka kuma ana umartar ku da kuzo fadar Mai Martaba Sarkin Kano a ranar Litinin 29 ga watan Ramadana 1440 A.H daidai da 3 ga watan Yuni, 2019 da karfe 11:00 na rana in Allah ya kai mu, don karbar umarnin Sarki ba tare da sabawa ko makara ba.

Dan haka muna fatan zaku shigo kamar yadda akayi umarni ba tare da sabawa ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel